COVID-19: Saudiyya za ta saka dokar kulle yayin hutun sallar Idi mai zuwa
Saudiyya za ta saka dokar zaman gida na awa 24 a dukkan sassan kasar na tsawon kwanaki biyar yayin hutun karamar sallah wato Eid al-Fitr domin yaki da Covid19 kamar yadda Maaikatar harkokin cikin gida ta sanar a ranar Talata.
Masarautar da Saudiyya wacce a halin yanzu ta fitar da alkalluma mafi yawa na wadanda suka kamu da cutar a yankin Gulf tana iya kokarinta ne domin dakile yaduwar cutar.
Za a sake saka dokar hana fita baki daya daga ranar 23 zuwa 27 ga watan Mayu, kamar yadda sanarwar da maaikatar ta fitar a wani kafar watsa labarai na kasar.
Wannan lokacin ya yi dai dai da lokacin da alummar musulmi ke yi bikin Sallah bayan kammala azumin watan Ramadan.

Asali: Twitter
DUBA WANNAN: Dokar kulle a Kano: 'Yan sanda suna sintiri a Kasuwar Kwari
An saka dokar kulle a mafi yawancin sassan kasar bayan bullar cutar amma a watan da ta gabata gwamnatin ta sassauta dokar inda aka bawa mutane damar fita daga 9 na safe zuwa 5 na yamma.
An bawa shaguna da kantina umurnin budewa sai dai a wasu wurarren da mutane da yawa ke hada hada a birnin Makka da aka samu yawaitar masu cutar duk da dokar kullen.
Maaikatar Lafiya ta kasar a ranar Talata ta sanar da cewa adadin wadanda COVID-19 ta kashe a kasar sun kai 264 kuma wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar ya kai 42,925 yayin da wadanda suka warke sun kai 15,257.
A watan Maris, Saudiyya ta dage yin aikin Umrah saboda fargabar yaduwar annobar da corona a birnin na Makka mai tsarki.
Kawo yanzu, Mahukunta a kasar ba su riga sun sanar ko za a gudanar da aikin hajji ba a wannan shekarar da ake shirin yi a watan Yuli amma sun sanar da alummar musulmi su jinkirta da yin shirye shiryen aikin hajjin.
A shekarar 2O19, kimanin mutane miliyan 2.5 ne suka tafi kasar ta Saudiyya domin sauke farali da Allah ya wajabtawa musulmi masu hali a kalla sau daya a rayuwarsu.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng