Buhari ya nada sabon shugaban NALDA

Buhari ya nada sabon shugaban NALDA

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin Paul Ikonne a matsayin babban sakataren Hukumar Habaka Filyen Noma na Kasa, NALDA.

Boss Mustapha, Sakataren Gwamnatin Tarayya, SGF, ne ya bayyana hakan a ranar Talata a birnin tarayya Abuja cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Direktan Watsa Labarai na ofishinsa, Wille Bassey.

A cewar Mr Mustapha, nadin da aka yi wa Mr Ikonne zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Yunin shekarar 2020 kuma nadin na shekara biyar kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Buhari ya nada sabon shugaban NALDA

Buhari ya nada sabon shugaban NALDA. Hoto daga Daily Trust
Source: UGC

DUBA WANNAN: Dokar kulle a Kano: 'Yan sanda suna sintiri a Kasuwar Kwari

Ya ce, "Kafin yanzu, Ikonne ya rike mukamai da dama a jihar Abia da suka hada da kwamishinan Kasa daga 2007 zuwa 2008 da kuma kwamishinan Ayyuka da Sufuri daga 2008 and 2009."

SGF din ya ce shugaban kasar ya taya Mr Ikonne murna bisa nadin da aka yi masa kuma ya umurce shi ya yi amfani da kwarewar da ya samu a ayyukan da ya yi a baya wurin sauke nauyin da aka daura masa.

A wani labarin, kun ji cewa tsohuwar 'Yar Majalisar Tarayya a jamhiriyya ta uku wadda ta wakilci mazabar Makurdi da Guma, Cif Rebbeca Apedzan ta kamu da cutar coronavirus kamar yadda New Telegraph ta ruwaito.

Hakan ya kawo adadin wadanda suka kamu da cutar a jihar ta Benue zuwa uku. Apezdan, wadda ta yi aiki a matsayin kwamishinan kasuwanci da masana'antu a lokacin mulkin Gwamna Goerge Akume a halin yanzu mamba ce a kwamitin amintattu na Hukumar Tattara Haraji na jihar, BIRS.

Gwamna Samuel Ortom ne ya bayyana hakan yayin jawabin da ya yi wa manema labarai jim kadan bayan ganawa da kwamitin kar ta kwana na Covid 19 a gidan gwamnati a Makurdi.

Gwamnan ya ce ya yi cudanya da mutum na farko da ya kamu da cutar a jihar a ranar Lahadi da ta gabata yayin wani taro duk da cewa ba su gwamutsu a wurin taron ba.

Amma duk da hakan ya yi alkawarin zai sake yin gwajin cutar ta Korona domin sanin matsayinsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel