Dattijon da ya rubuta Alqur’ani gaba daya da hannunsa ya rasu a Maiduguri

Dattijon da ya rubuta Alqur’ani gaba daya da hannunsa ya rasu a Maiduguri

- Wani dan Najeriya a shafin sadarwa na Twitter mai amfani da sunan @official_mukhthar, ya sanya hoton wani dattijo da ya riga mu gidan gaskiya.

- Matashin ya ce dattijon ya rubuce Al-Qur'ani kakaf da hannunsa gabanin ajali ya katse masa hanzari

- Daga nan sai saurayin ya yi addu'ar Allah ya sakawa dattijon da babban matsayi na Aljannah

Wani saurayi mai amfani da sunan @official_mukhthar a dandalin sada zumunta na Twitter, ya yada labarin mutuwar wani dattajo da ya har ya wuce Gwani ya zama Gangaran wajen hidimtawa Al-Qur'ani.

Saurayin mai suna Mukhtar, ya ce dattijon mai suna Sheikh Goni Modu Goni Kolo, ya rubuce Al-Qur'ani kakaf da hannunsa a yayin rayuwarsa.

Babu shakka ajali ko kuma yawan shekaru su na iyakance burikan mutane da dama, ta yadda ba sa iya cimma wasu bukatunsu kamar yadda inda sun kasance matasa.

Duk da hakan, kudira ta Ubangiji ta kan sa wasu tsoffin mutane su cimma burikansu musamman idan sha'anin ya dangaci faranta wa Mahallicinsu.

KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa ba mu yanke shawarar dage zaben gwamnan Edo da Ondo ba - INEC

Marigayi Sheikh Goni Modu ya shahara wajen rubuta Al-Qur'ani kakaf da hannunsa, lamari da ke iya daukar wasu mutanen watanni da su ka sadaukar da kai wajen aiwatar da hakan.

Matashin bayan ya ba da rahoton mutuwar dattijon kwanaki kadan da suka gabata, ya kuma roki Mai Duka ya yi wa tsohon sakayya da mafi girman masaki a cikin gidan Aljanna.

Marigayin ya kasance bajimin malami mai karantarwa a daya daga cikin makaruntun tsangaya na Maiduguri a jihar Borno da ke yankin Arewa maso Gabas a Najeriya.

Hakazalika, wata matashiyar budurwa mai suna Alim Joda ta wallafa labarin mahaifinta a kafar sada zumuntar zamani.

Alim Joda ta ce duk da mahaifinta na da shekaru 96 a duniya, yana sauke Qur'ani sau daya a duk bayan kwana uku sannan yana iya azumin watan Ramadan.

Ba a nan ya tsaya ba, yana limancin sallar taraweehi a kowacce rana kamar yadda ta bayyana.

Sau da yawa ana kallon tsofaffi a matsayin mutane masu rauni kuma basu iya yi wasu ayyuka saboda shekarunsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel