Dalilin da ya sa ba mu yanke shawarar dage zaben gwamnan Edo da Ondo ba - INEC

Dalilin da ya sa ba mu yanke shawarar dage zaben gwamnan Edo da Ondo ba - INEC

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC, ta ce har yanzu ba ta yanke shawarar dage zaben gwamna a jihohin Edo da Ondo ba wanda ta tsara gudanarwa watan Satumba da kuma Oktoba na bana.

Duba da yadda annobar korona ta tsaida al'amura a fadin duniya ba ma a Najeriya kadai ba, ya sanya ake rade-radin cewa babu lallai zaben ya tabbata a bana.

Sai dai hukumar a ranar Litinin ta sake kawar da shakku da cewa, za a gudanar da zaben gwamna a jihohin Edo da Ondo a ranakun 19 ga watan Satumba da kuma 10 ga watan Oktoba na 2020 kamar yadda ta tsara tun a baya.

Sanarwar hakan ta fito ne daga bakin wani kakakin kwamishinan hukumar, Festus Okoye, lamarin da ya ce dage zaben zai iya sanya INEC ta rasa 'yancin zabar ranakun zabe a lokuta na gaba.

Shugaban hukumar INEC; Farfesa Mahmoud Yakubu

Shugaban hukumar INEC; Farfesa Mahmoud Yakubu
Source: Twitter

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa, tun a watan Fabrairun 2020, INEC ta tsaida wannan ranaku na gudanar da zaben gwamnan jihar Edo da kuma na Ondo.

KARANTA KUMA: Sunayen jakadu 42 da Buhari ya ke neman majalisar dattawar ta amince da su

Da ya ke ganawa da manema labarai na gidan Talabijin din ARISE, Mista Okoye ya ce INEC ta na sane da irin ta’adin da cutar korona ta ke yi, kuma su na bibiyar kokarin da gwamnati da muhukuntan lafiya ke yi a kai.

Mista Okoye ya ambaci kundin tsarin mulki na 1999, wanda ya baiwa INEC 'yancin gudanar da zabe gabanin kwana 150 kuma kada ya yi kasa da kwanaki 30 zuwa lokacin karewar wa'adin wanda yake kan mukami.

Okoye ya ce: “Idan lokaci ya zo kuma akwai bukatar a yi wa jadawalin kwaskwarima, za mu sanar da jama’a kamar dai yadda mu ka saba sanar da su ta hanyoyin da suka dace.”

Ya karkare jawabin na sa da cewa: “A daidai wannan lokaci, za mu cigaba da lura da lamarin da kyau tare da hada kai da masu ta-cewa wajen yaki da annobar korona.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel