Katsina: Sarkin Daura, Umar Faruk, ya warke sarai

Katsina: Sarkin Daura, Umar Faruk, ya warke sarai

- Sarkin Daura, Mai Martaba Alhaji Umar Faruk Umar da aka kwantar a asibiti a Katsina ya samu sauki

- Kakakin fadar sarkin, Usman Ibrahim ya tabbatar da sahihancin bidiyon da ke yawo na mai martaba a harabar asibitin yana karbar gaisuwar mutane

- Ibrahim ya ce mai martabar ya samu sauki sosai kuma yana huta wa ne yana jirar likitoci su sallame shi

Mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar da aka kwantar a asibitin kwararru na gwamnatin tarayya da ke Katsina tun ranar 5 ga watan Mayu sakamakon rashin lafiya da ba a bayyana irin ta ba ya warke inda har ya karbi gaisuwa a harabar asibitin.

Wani bidiyo da ke yawo a dandalin sada zumunta ya nuna sarkin yana zaune a kan farar kujera ta roba yayin da mutane ke zuwa gabansa suna fadi suna gaisuwa tare da fadawa a tare da shi.

Katsina: Sarkin Daura, Umar Faruk, ya warke sarai
Katsina: Sarkin Daura, Umar Faruk, ya warke sarai. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Dokar kulle a Kano: 'Yan sanda suna sintiri a Kasuwar Kwari

Mai magana da yawun masarautar Dauram, Alhaji Usman Ibrahim ya tabbatar da sahihancin bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta.

Usman Ibrahim ya ce, "Tabbas wannan bidiyon da ke yawo, Mai martaba Sarkin Daura Alhaji Umar Faruk ne, ya samu sauki sosai, huta wa ya ke yi yana jiran likitoci su sallame shi."

Wasu mutane da dama na yada rade–radin cewa cutar korona mai shake numfashi ne ta kama mai martaba amma Usman Ibrahim ya ce hakan ba gaskiya bane.

Ya dai ce mai martaba ya yi rashin lafiya kuma ya samu sauki.

Ya kara da cewa, "Sarkin na godiya bisa adduoin da alumma suke masa kuma ya dauki wannan rashin lafiyar tasa a matsayin jarrabawa daga Allah."

Idan dai ba a manta ba a ranar 7 ga watan Mayu ne aka garzaya da mai martaba zuwa Asibitin Kwararru ta gwamnatin tarayya da ke Katsina a kan wani rashin lafiya da ba a bayyana ba.

Daily Trust ta ruwaito cewa wata majiya daga iyalan sarkin ta ce an dauki mai martaba daga fadarsa a Daura zuwa Katsina inda aka kwantar da shi a sashin majinyatan da ke bukatar kulawa sosai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel