Magajin Abba Kyari: Rashin tabbacin da ke tattare da nadin farfesa Gambari

Magajin Abba Kyari: Rashin tabbacin da ke tattare da nadin farfesa Gambari

Rashin tabbaci na tattare da nadin Farfesa Ibrahim Gambari a matsayin sabon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A wata takarda da Sarkin Ilori, Alhaji Sulu-Gambari, a wata takarda da ya fitar a ranar Talata, ya mika godiyarsa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan nada Gambari a sabon mukamin.

Kafofin yada labarai sun ci gaba da wallafa yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Farfesa Gambari a matsayin magajin Abba Kyari.

Jaridar yanar gizo ta The Cable ta wallafa cewa, "Za a bayyana Gambari a matsayin sabon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa a ranar Laraba".

Ta wallafa cewa, "Duk da ba a tabbatar da nadin ba, jaridar ta samu bayani daga wata majiya ta fadar shugaban kasar cewa Gambari zai maye gurbin marigayi Kyari wanda korona ta kashe a watan da ya gabata."

Magajin Abba Kyari: Rashin tabbacin da ke tattare da nadin farfesa Gambari

Magajin Abba Kyari: Rashin tabbacin da ke tattare da nadin farfesa Gambari. Hoto daga jaridar New Telegraph
Source: UGC

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Buhari ya nada sabon shugaban ma'aikatan fadarsa

Amma kuma duk da rahoto da kuma sakon godiyar da sarkin ya mika wa shugaban kasar, fadar shugaban kasar ba ta wallafa wani bayani na tabbacin nadin ba.

Hakazalika, fadar shugaban kasar ba ta musanta lamarin ba.

Femi Adesina da Malam Garba Shehu, masu magana da yawun shugaban kasa Muhammadu Buhari ba su bada tabbaci ko musanta nadin ba.

Shehu dai ya yi martani mara tsawo a kai inda ya ce, "Ba a sanar da ni ba."

A ranar 17 ga watan Afirilun 2020 ne Kyari ya ce ga garinku sakamakon cutar korona.

Amma kuma da jaridar The Punch ta zanta da wata majiya daga fadar sarkin, ta ce fadar ba ta samu wata takardar tabbacin nadin Gambari ba. Hakazalika ba ta samu sanarwa ta musamman daga hadiman shugaban kasar.

Tsohon sakataren majalisar dinkin duniya, Farfesa Ibrahim Gambari ya zama magajin marigayi Abba Kyari.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada tsohon sakataren majalisar dinkin duniyan a matsayin shugaban ma'aikatan fadar sa.

Gambari dan asalin jihar Kwara ne kuma ya yi tsohon ministan harkokin waje tsakanin 1984 zuwa 1985.

Farfesan na da babbar shaidar kwarewa da jajircewa. Yana da shekaru 78 a duniya a yanzu da ya maye gurbin marigayi Abba Kyari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel