COVID-19: Hauhawar mace-mace a jihohin Kano, Jigawa da Yobe na ci gaba da tada hankula

COVID-19: Hauhawar mace-mace a jihohin Kano, Jigawa da Yobe na ci gaba da tada hankula

Hauhawar mace-mace a jihohin Kano, Jigawa da Yobe a makon karshe na watan Afirilu da farko Mayu na ci gaba da girgiza zukatan 'yan Najeriya da ke fuskantar barkewar annobar korona.

Kamar yadda rahoto ya bayyana, rayuka 15 aka rasa a cikin kwanaki biyu a jihar Kano yayin da jihar Jigawa ta rasa rayuka 100 a cikin kwanaki uku.

Daruruwan rayuka kuwa sun salwanta a cikin kwanaki kalilan a kananan hukumomin Potiskum, Bade da Nguru a jihar Yobe.

Jimillar rayukan da aka rasa a jihohin ya zarta yawan wadanda cutar korona ta halaka a fadin kasar nan.

Babban abun tashin hankali kuwa shine yadda hukumomi suke bayyana cewa basu san da mace-macen ba.

Hakazalika, martanin hukumomin jihohin ya kama daga musanta lamarin zuwa cewa ana zuzuta mace-macen, jaridar Daily Trust ta wallafa.

Yayin da har yanzu hukumomi a jihar Kano ba su bankado silar mace-macen ba duk da tallafin jami'an gwamnatin tarayya, jihohin Jigawa da Yobe sun ce dama can ana irin wadannan mace-macen a irin lokacin nan duk shekara.

COVID-19: Hauhawar mace-mace a jihohin Kano, Jigawa da Yobe na ci gaba da tada hankula
COVID-19: Hauhawar mace-mace a jihohin Kano, Jigawa da Yobe na ci gaba da tada hankula. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Abinda yasa na daina sumbata da rungumar mata a fim - Ali Nuhu

Sun kafa kwamitocin bincike don gano halin da ake ciki. Amma kuma rahotanni sun nuna cewa, zazzabi mai zafi, ciwon sukari da hawan jini ke kawo mace-macen.

Rahoton ya kara da bayyana cewa, da yawa daga cikin wadanda ke rasuwar duk tsofaffi ne wadanda ke da wasu cutuka tuntuni.

Amma kuma rahotannin da aka fara samu sun bayyana cewa mace-macen na aukuwa ne ba saboda kwayar cutar korona ba, lamarin da ya kwantar da hankulan jama'a.

Wasu rahotannin na nuna cewa rashin isassun cibiyoyin kiwon lafiya na daga cikin abinda ya kawo mace-macen. Ma'aikatan lafiya kuwa hankalinsu ba ya kan majinyatan don gudun kwasar muguwar annobar.

Wadannan mace-macen sun fallasa rashin ingancin cibiyoyin lafiyarmu da rashin kayan aikin da ma'aikatan lafiyar kasar nan ke fuskanta.

Tsari da kiyaye yaduwar cutar na daga cikin hanyoyin shawo kan wannan muguwar annobar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel