Abinda yasa na daina sumbata da rungumar mata a fim - Ali Nuhu

Abinda yasa na daina sumbata da rungumar mata a fim - Ali Nuhu

Fitaccen jarumin fina-finai, Ali Nuhu ya ce ya tuba da sumbata ko rungumar mata a cikin fina-finan kudancin Najeriya.

Ya ce ya daina ne saboda hakan bai dace da al'adu da addinin Islama ba.

A hirar da jarumin ya yi da BBC a shafinsa na Instagram a ranar Talata, fitaccen jarumin ya ce ba zai daina sana'ar fim ba.

A yayin da jarumin ke amsa tambayoyi da jama'a ke masa, wani ya tambayesa a kan yadda yake fuskantar yanayin da zai iya kai shi ga sumba ko rungunar mace a fina-finan Nollywood, jarumin ya ce a da ne yake runguma tare da sumbatar mata.

Kamar yadda Ali Nuhu ya bayyana, korafi da koken mutane ne kuma a matsayinsa na jakadan arewa da addininsa yasa dole ya bar hakan.

Jarumin ya bayyana cewa babu wanda ya taimaka mishi da ko sisi a lokacin da ya fara shirya fina-finai.

Abinda yasa na daina sumbata da rungumar mata a fim - Ali Nuhu
Abinda yasa na daina sumbata da rungumar mata a fim - Ali Nuhu. Hoto daga BBC
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Buhari ya nada sabon shugaban ma'aikatan fadarsa

Jarumin ya ce ba zai iya kayyade adadin fina-finan da ya fito ba saboda yawansu.

Jarumin, wanda ake yi wa lakabi da Sarki a fagen fina-finan Kannywood, ya ce harkar fim ce abin da ya fi sani a rayuwarsa tun yana matashi har yanzu.

Hakan ne yasa bashi da burin da ya wuce ya ga an ci gaba da samun sauyi mai kyau a masana'antun fina-finan.

Jarumi Ali Nuhu ya kwashe sama da shekaru 20 yana taka rawar gani a fina-finan Kannywood da Nollywood, ya lashe lambobin yabo a ciki da wajen Najeriya.

A wani labari na daban, tsohon sakataren majalisar dinkin duniya, Farfesa Ibrahim Gambari ya zama magajin marigayi Abba Kyari.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada tsohon sakataren majalisar dinkin duniyan a matsayin shugaban ma'aikatan fadar sa.

Gambari dan asalin jihar Kwara ne kuma ya yi tsohon ministan harkokin waje tsakanin 1984 zuwa 1985. Farfesan na da babbar shaidar kwarewa da jajircewa.

Yana da shekaru 78 a duniya a yanzu da ya maye gurbin marigayi Abba Kyari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel