Da duminsa: Gwamnatin Kaduna ta sallami masu cutar Korona 12, 11 Almajirai ne

Da duminsa: Gwamnatin Kaduna ta sallami masu cutar Korona 12, 11 Almajirai ne

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da sallamar masu cutar Coronavirus 12 dake jinya a cibiyar killacewanta a ranar Talata, 12 ga watan Mayu, 2020.

11 cikin wadanda aka sallama yan makarantan Allo ne wadanda akafi sani da Almajirai.

Gwamnan jihar, Nasir Ahmed El-Rufa'i da kansa ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita inda yace:

"An sallami masu jinyan cutar COIVD-19 12 yau, cikin akwai Almajirai 11. Yanzu jihar Kaduna ta sallami jimillan mutane 27."

A daren jiya, hukumar NCDC ta sanar da kamuwar sabbin mutane 13 da cutar Korona a jihar Kaduna. Jimillan masu cutar yanzu 111.

KU KARANTA: Barayi sun balle tare da shiga wani ofishi a ginin majalisar dattawan Najeriya da ke Abuja

Gabanin sanarwan gwamnan Kaduna, Gwamnatin jihar Sokoto ta sanar da sallamar masu fama da cutar nan mai toshe numfashi watau Coronavirus 22 cikin 75 dake jinya a cibiyar killacewa dake unguwar Amanawa.

Shugaban kwamitin yaki da da cutar COVID19 na jihar, wanda shine kwamishanan lafiya, Dr Ali Inname, ya bayyana hakan yayinda yake hira da manema labarai a jihar ranar Talata.

Dr Inname ya ce mutane 106 ne suka kamu da cutar kawo ranar 11 ga Mayu 106 ne, kuma 12 sun rigamu gidan gaskiya.

Yace: "Daga cikin mutane 75 dake da cutar yanzu, mun samu nasarar sallaman mutane 22 da gwaji biyu daban-daban ya nuna sun waraka daga COVID-19."

"Jimillar wadanda aka sallama yanzu 41 cikin 106 da suka kamu da cutar a jihar."

"Bugu da kari, an samu karin wadanda suka mutu ya karu da daya yau."

A daren jiya Litinin, an samu karin sabbin mutane 242 da suka kamu da cutar a Najeriya, kamar da hukumar NCDC ta sanar.

Kawo yanzu, mutane 4641 ne ya tabbata sun kamu da cutar a Najeriya. Yayinda 902 sun samu waraka kuma an sallamesu, 150 sun rigamu gidan gaskiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel