Buhari ya maye gurbin mamacin da ya nada mukami a gwamnatinsa

Buhari ya maye gurbin mamacin da ya nada mukami a gwamnatinsa

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya maye gurbin Tobias Okwuru, mamacin da ya nada a matsayin mamba a hukumar daidaito a rabon guraben aikin tarayya a tsakanin 'yan kasa (FCC) sati biyu da suka gabata.

Sunan marigayi Okwuru na daga cikin jerin sunayen mutane 37 da shugaba Buhari ya aikawa majlaisar dattijai domin amincewa da su a matsayin mambobin hukumar FCC.

Batun nadin mamaci a matsayin mamba a FCC ya jawo barkewar cece-kuce a tsakanin 'yan Najeriya.

A cikin wata wasika da shugaban majalisar dattijai, Ahmed Lawan, ya karanta a zauren majalisar ranar Talata, ya ce shugaba Buhari ya bukaci sauya sunayen mutane hudu da suka hada da Okwuru.

"Kamar yadda doka ta bani dama a sashe na 156(1) na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999, ina son sauya sunayen mutane hudu daga cikin sunayen mutanen da na aiko domin amincewa da su a matsayin mambobin hukumar FCC ," a cewar wasikar.

Sauran mutanen da shugaba Buhari ya maye sunayensu bayan marigayi Okwuru sune; Moses A (daga jihar Delta), Afamefuna Osi (daga jihar Ebonyi), Wasiu Kayode (daga jihar Legas) da Alakayi Mamman (daga jihar Nasarawa).

Buhari ya maye gurbin mamacin da ya nada mukami a gwamnatinsa
Buhari
Asali: Twitter

Bayan hakan, majalisar dattijai ta tabbatar da samun wasikar shugaban kasa, Muhammad Buhari, a kan neman amincewa da nadin Jumai Audi a matsayin shugabar hukumar NLRC (Nigerian Law Reform Commission).

Kazalika, shugaba Buhari ya nemi majalisar ta amince na nadin Ebele Chima, Bassey Abia, da Mohammed Ibraheem a matsayin kwamishinoni da zasu wakilcin yankunan da suka fito a hukumar NLRC.

DUBA WANNAN: Muhimman abubuwa 4 da gwamonin zasu tattauna yayin ganawarsu ranar Laraba

A wata wasikar da Buhari ya aikawa majalisar, ya nemi amincewarta da Diana Okonta (daga kudu maso kudu), Ya'ana Yaro (daga arewa maso gabas) a matsayin darektoci a hukumar NDIC (Nigeria Deposit Insurance Corporation).

Yahaya Abdullahi, barden majalisar dattijai, ya bukaci majalisar ta gaggauta amincewa da tabbatar da sunayen dukkan mutanen da shugaba Buhari ya aiko.

A ranar Litinin ne Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da nadin Mohammed Bello Shehu, a matsayin sakataren hukumar kasafin kudaden haraji da gwamnatin tarayya ta samu.

Shehu, wanda nadinsa ya fara aiki a ranar 19 ga watan Maris, zai shafe zangon farko mai wa'adin shekaru biyar a hukumar RMAFC tare da zabin sabunta nadinsa a zango na biyu idan shugaban kasa ya ga dama.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel