Mutum 42,000 ne suka yi hijira daga jihohi 3 na yankin arewacin Najeriya - UNHCR

Mutum 42,000 ne suka yi hijira daga jihohi 3 na yankin arewacin Najeriya - UNHCR

Sama da jama'a 42,000 ne suka bar yankin arewacin Najeriya sakamakon harin 'yan bindiga. Sun tsere zuwa iyakar Nijar a cikin makonni kadan da suka gabata, hukumar kula da 'yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya (UNHCR) ta sanar a ranar Talata.

Ana rikici a yankin ne sakamakon hargitsi da hayaniya a kan filaye da ruwa, ballantana tsakanin makiyaya da manoma, jaridar Daily Trust ta wallafa.

Majalisar dinkin duniya ta ce, "Da yawa daga cikinsu mata ne kananan yara". An bar su tsallakawa zuwa jamhuriyar Nijar duk kuwa da cewa iyakokin kasar a rufe suke sakamakon annobar korona.

"Rashin zaman lafiya da hargitsin da ke aukuwa a yankin arewa ya tilasta a kalla mutum 23,000 neman mafaka a kasar Nijar a watan da ya gabata," cibiyar ta ce a wata takarda da ta fitar.

"Sakamakon tsoro da rashin tsaro a yankunan iyakokin, wasu mutum 19,000 amma asalin 'yan kasar Nijar sun kara shigewa cikin kasar," ta kara da cewa.

Hakan ce ta kai yawan 'yan gudun hijirar da suka bar kasar nan zuwa jamhuriyar Nijar suka kai 60,000 tun daga watan Afirilun shekarar da ta gabata.

Gudun hijira: UNHCR ta bayyana adadin jama'ar da suka bar arewacin Najeriya zuwa Nijar
Gudun hijira: UNHCR ta bayyana adadin jama'ar da suka bar arewacin Najeriya zuwa Nijar. Hoto daga jaridar Daily Trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Dokar kulle a Kano: 'Yan sanda suna sintiri a Kasuwar Kwari

Wannan gudun hijirar kwanan nan ta biyo bayan zubda jinin da ke aukuwa a wasu jihohin Najeriya da suka hada da Katsina, Sokoto da Zamfara, a cewar cibiyar.

Ta kara da cewa jihar da ta fi fuskantar kalubale da zubda jini sakamakon aikin 'yan ta'addan ita ce jihar Katsina.

Mummunan harin da aka taba kai wa jihar kuwa shine na ranar 18 ga watan Afirilu wanda aka rasa rayuka 47.

Kamar yadda takardar ta sanar, "Wadanda suka bar yankunan sakamakon tashin hankalin kashe-kashe, garkuwa da mutane da kuma fashi a kauyukansu suna da tarin yawa."

A dukkan yawan 'yan gudun hijiarar, jamhuriyar Nijar ce ta bai wa kusan rabin miliyan daga cikinsu masauki. Sun hada da 'yan gudun hijira da Mali, Burkina Faso da kuma Nijar, kamar yadda majalisar dinkin duniya ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164