Da duminsa: An sallami masu Coronavirus 22 a birnin Shehu bayan samun waraka

Da duminsa: An sallami masu Coronavirus 22 a birnin Shehu bayan samun waraka

Gwamnatin jihar Sokoto ta sanar da sallamar masu fama da cutar nan mai toshe numfashi watau Coronavirus 22 cikin 75 dake jinya a cibiyar killacewa dake unguwar Amanawa.

Shugaban kwamitin yaki da da cutar COVID19 na jihar, wanda shine kwamishanan lafiya, Dr Ali Inname, ya bayyana hakan yayinda yake hira da manema labarai a jihar ranar Talata.

Dr Inname ya ce mutane 106 ne suka kamu da cutar kawo ranar 11 ga Mayu 106 ne, kuma 12 sun rigamu gidan gaskiya.

Yace: "Daga cikin mutane 75 dake da cutar yanzu, mun samu nasarar sallaman mutane 22 da gwaji biyu daban-daban ya nuna sun waraka daga COVID-19."

"Jimillar wadanda aka sallama yanzu 41 cikin 106 da suka kamu da cutar a jihar."

"Bugu da kari, an samu karin wadanda suka mutu ya karu da daya yau."

Kwamishanan ya kara da cewa kashi 30% mata ne yayinda 70% maza ne.

Ya ce jihar ta bibiyi mutane 874 kuma an gwada 431 cikinsu.

A daren jiya, hukumar NCDC ta sanar da cewa ba'a samu kamuwar sabbin mutane da cutar Korona a jihar Sokoto ba amma jimillan masu cutar yanzu 106.

KU KARANTA: Da duminsa: Gwamnatin Kaduna ta sallami masu cutar Korona 12, 11 Almajirai ne

A daren jiya Litinin, an samu karin sabbin mutane 242 da suka kamu da cutar a Najeriya, kamar da hukumar NCDC ta sanar.

Kaow yanzu, mutane 4641 ne ya tabbata sun kamu da cutar a Najeriya. Yayinda 902 sun samu waraka kuma an sallamesu, 150 sun rigamu gidan gaskiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel