COVID-19: Mutum 6 sun sake rasuwa a jihar Kano

COVID-19: Mutum 6 sun sake rasuwa a jihar Kano

Ma'aikatar lafiya ta jihar Kano ta sanar da rasuwar wasu mutum 6 a jihar sakamakon annobar Coronavirus.

A shafinta na twitter, ma'aikatar lafiyar ta kara da cewa majinyata 63 ne suka warke sarai daga cutar kuma an sallamesu.

Daga cikin wadanda aka sallama akwai mutum na farko da ya kamu da cutar a jihar, Kabiru Rabiu, tsohon ambasada. An zargi Rabiu da boye gaskiya a kan tarihin tafiye-tafiyensa a yayin da ya garzaya asibiti a jihar.

A ranar Litinin ne hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa ta sanar da samun sabbin mutum 242 masu dauke da cutar korona a fadin kasar nan. Jihar Kano ce ke da sabbin kamu har 64, kamar yadda jaridar Premium Times ta wallafa.

NCDC ta sanar da rasa karin rayuka 10 a fadin kasar nan sakamakon cutar amma bata sanar da jihohin ba.

COVID-19: Mutum 6 sun sake rasuwa a jihar Kano

COVID-19: Mutum 6 sun sake rasuwa a jihar Kano. Hoto daga The Cable
Source: Facebook

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Buhari ya nada sabon shugaban ma'aikatan fadarsa

Amma kuma jihar Kano ta tabbatar da cewa mutum shida ta sake rasa wa a sakamakon annobar.

A yayin da Legas ta kasance jihar da ta fi kowacce yawan masu cutar, yawan masu cutar a jihar Kano yana hauhawa a yayin da aka sassauta dokar hana zirga-zirga a ranakun Litinin da Alhamis.

Hakazalika, gwamnatin jihar Kano ta tsawaita dokar hana zirga-zirga a jihar na mako daya don dakile yaduwar muguwar cutar.

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da raba takunkumin fuska miliyan biyu a ranar Litinin.

Gwamnatin jihar ce ta samar da miliyan daya yayin da kananan hukumomi 44 na jihar suka samar da sauran miliyan dayan.

A wani labari na daban, tsohon sakataren majalisar dinkin duniya, Farfesa Ibrahim Gambari ya zama magajin marigayi Abba Kyari.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada tsohon sakataren majalisar dinkin duniyan a matsayin shugaban ma'aikatan fadar sa.

Gambari dan asalin jihar Kwara ne kuma ya yi tsohon ministan harkokin waje tsakanin 1984 zuwa 1985. Farfesan na da babbar shaidar kwarewa da jajircewa.

Yana da shekaru 78 a duniya a yanzu da ya maye gurbin marigayi Abba Kyari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel