Allah Ya jikan Musulmi: Jahar Zamfara ta yi rashin wasu manyan jami’an gwamnati

Allah Ya jikan Musulmi: Jahar Zamfara ta yi rashin wasu manyan jami’an gwamnati

Gwamnatin jahar Zamfara ta sanar da mutuwar manyan sakatarorinta guda biyu a cikin kwanaki biyu sakamakon wata yar gajeruwar rashin lafiya da suka yi fama da ita.

Jaridar Punch ta ruwaito manyan jami’an gwamnatin da suka mutu sun hada da Alhaji Yawale Dango, babban sakatare a ofishin shugaban ma’aikatan jahar.

KU KARANTA: Kowa ya raina gajere ya taka kunama: El-Rufai ya fadi sunan jagoran tafiyarsu ta ‘Kungiyar gajerun Najeriya’

Sai kuma Alhaji Ahmed Sale, babban sakatare a ma’aikatan gidaje da cigaban biranen jahar Zamfara. Sale ya rasu a ranar Talata, yayin da Dango ya rasu a ranar Larabar da ta gabata.

Tuni an yi ma mamatan biyu jana’iza tare da binnesu kamar yadda dokokin addinin Musulunci suka tanadar.

Shi ma a sakon ta’aziyya da ya fitar ta bakin hadiminsa a bangaren watsa labaru, Zailani Baffa, gwamnan jahar Zamfara, Bello Matawalle ya yi addu’ar; Allah Ya jikansu.

“Allah Ya shigar da su Aljanna, Ya baiwa iyalansu hakurin rashi.” Inji shi.

Allah Ya jikan Musulmi: Jahar Zamfara ta yi rashin wasu manyan jami’an gwamnati

Matawalle Hoto: Pulse
Source: UGC

Gwamna Matawalle ya bayyana mutanen biyu a matsayin hazikai, kuma jajirtattun ma’aikata wanda suka sadaukar da kawunansu wajen hidimta ma jahar Zamfara.

An samu mace macen manyan mutane da dama a yankin Arewacin Najeriya a yan kwanakin nan, tun daga jahar Kano, zuwa Jigawa, Bauchi, Borno, Sokoto da kuma jahar Zamfara.

A makon da ta gabata ne mai martaba Sarkin Kano ya yi rashin kawunsa, Iyan Kano, haka zalika Gwamna Tambuwal na sakkwato ya yi rashin kawunsa da abokin aikinsa kwamishina.

A Bauchi an samu rasuwar Matawallen Katagum Dahiru Saleh, mahaifiyar Ministan ilimi Adamu Adamu, Dan iyan Katagum Umaru Yakubu.

A Borno ma mahaifin tsohon gwamna Ali Modu Sheriff ya rasu, kamar yadda mahaifyar Laftanar Janar Buratai ta rasu, Sarkin Bama, Kyari Ibn Umar da dai sauransu.

A hannu guda kuma, Gwamnatin jahar Gombe ta sanar da samun mutum na farko daya mutu a sakamakon mugunyar cutar nan ta Coronavirus mai sarke numfashin dan Adam a jahar.

Premium Times ta ruwaito shugaban kwamitin yaki da cutar COVID-19 na jahar, Idris Muhammad ne ya bayyana haka yayin da yake gabatar da jawabi game da aikin kwamitinsu.

Idris ya bayyana mamacin a matsayin dan shekara 50, wanda yace cutar ciwon siga na damunsa, kuma ya rasu ne da misalin karfe 4 na rana a ranar Lahadi, 10 ga watan Mayu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel