WHO ta lissafa abubuwa 6 Buhari da sauran shuwagabanni za su yi kafin su cire dokar kulle gaba daya

WHO ta lissafa abubuwa 6 Buhari da sauran shuwagabanni za su yi kafin su cire dokar kulle gaba daya

- Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta fitar da wasu sharudda shida da dole sai shugabannin duniya sun cika kafin su cire dokar kulle da suka sanya saboda cutar korona

- Shugaban WHO Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce shawarar cire dokar kulle dole ta dogara a kan manufar tsare lafiyar al'umma

- Daya daga cikin sharuddan da WHO ta gindaya sun hada da tabbatar da inganci na karfin tsarin kiwon lafiya wajen lalube, gwaji da killace dukkanin wadanda cutar korona ta harba

A halin yanzu cutar korona ta harbi sama da mutum miliyan hudu a dukkanin yankunan da cutar ta bulla a fadin duniya.

Alkaluman mahukuntan lafiya sun nuna cewa, akwai mutum 4,269,200 da cutar ta harba kuma mutum 287,504 sun halaka a sanadiyar cutar.

Sai dai babu shakka an samu mutum 1,533,808 da suka warke bayan kamuwa da ita a fadin duniya.

Bayan shafe tsawon makonni ana zaman dirshan babu fita tare da takaice zirga-zirga a yunkurin dakile yaduwar cutar korona, a yanzu kasashe da dama sun fara sassauta dokar kulle wadda ta hana mutane fita a baya.

Kasashe da dama a yanzu irinsu Jamus, Birtaniya da sauransu, bayan sassauta dokar kulle sun kuma fara shirye-shiryen dawo da harkoki da ci gaba da gudanar da al'amuran yau da kullum.

Haka kuma, sannu a hankali Najeriya, Ghana da kuma Afirka ta Kudu, sun fara sassauta dokar kulle da ta kuntatawa al'ummominsu a yayin da garin neman gira ake kokarin a rasa idanu.

Shugaban WHO; Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus

Shugaban WHO; Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus
Source: UGC

Babu shakka dokar kulle da hana fita ta kuntatawa al'ummomi da dama gami da haddasa durkushewar tattalin arziki. Sai dai wasu na ganin cewa cire dokar akwai hadari.

Yayin da shugabannin duniya suka fara yunkurin cire dokar kullen, Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta fitar da wasu ka'idodi 6 da ya kamata a yi la'akari da su kafin daukar wannan mataki.

KARANTA KUMA: Babban Editan wata shahararriyar jarida ya rasa mahaifinsa a Kano

Darakta Janar na WHO, Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ba shawarwari a kan matakai da kuma lokacin da ya dace a cire dokar kullen da aka shimfida da manufar dakile yaduwar cutar korona.

Dr Adhanom ya ce abu na farko kuma mafi a'ala gabanin cire dokar kullen, shi ne a tabbatar da tsaron lafiyar al'umma kuma a samu cikakkiyar masaniya kan yadda cutar ta ke da duk wasu halayenta.

1. Dakile yaduwar cutar

Dr Ghebreyesus ya ce dole ne shugabannin duniya su tabbatar cewa sun shawo kan yaduwar cutar kafin su cire dokar kulle gaba daya.

2. Ingancin tsarin kiwon lafiya

Sharadi na biyu a cewar Daraktan na WHO, shi ne tabbatar da ingancin tsarin kiwon lafiya mai ikon lalube, gwaji, da kuma killace duk masu dauke da kwayoyin cutar.

3. Rage hatsarin barkewar cutar

Dole ne shugabanni su tabbatar cewa an rage girman hadarin barkewar cutar a wurare na musamman kamar wuraren kiwon lafiya da gidajen raino.

4. Matakan kariya a wuraren taron jama'a

An shawarci shugabannin duniya su tabbatar da tanadin ingatattun matakai na kariya a wuraren da jama'a ke taruwa, kamar makarantu, wuraren aiki, wuraren ibada, da kuma sauran wurare da ya zama wajibi kuma akwai bukatar mutane su ziyarta.

5. Kula da hatsarin cutar yayin shigo da kayayyaki

Dole ne kuma shugabannin duniya su tabbatar da cewa ana sanya lura a kan hatsarin cutar yayin shigo da kayayyaki

6. Ilmantar da al'umma

A karshe, dole ne shugabannin duniya su tabbatar da cewa al'ummominsu suna da cikakken ilimi a kan cutar korona da duka wasu halayenta. Su kuma kasance sun yi riko da sabbin dabi'u na kare kai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel