Dokar kulle a Kano: 'Yan sanda suna sintiri a Kasuwar Kwari

Dokar kulle a Kano: 'Yan sanda suna sintiri a Kasuwar Kwari

'Yan sanda a jihar Kano a ranar Litinin sun rufe dukkan kofofin shiga Kasuwar Kwari da ke Kano domin cigaba da tabbatar da dokar kulle da Shugaba Muhammadu Buhari ya saka a jihar domin dakile yaduwar korona kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wa'adin kullen na sati biyu zai kare ne a jiya Litinin 11 ga watan Mayu dai kuma Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya kuma tsawaita dokar kulle da sati daya.

Adadin mutanen da aka tabbatar sun harbu da cutar korona a jihar sun kai 666 a ranar Litinin 11 ga watan Mayun shekarar 2020.

Dokar kulle a Kano: 'Yan sanda suna sintiri a Kasuwar Kwari

Dokar kulle a Kano: 'Yan sanda suna sintiri a Kasuwar Kwari. Hoto daga Daily Trust
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Korona: Ta harbi karin mutum 242 a Najeriya, 64 a Kano, 49 a Katsina, 13 a Kaduna

Jami'an tsaro a ranar Alhamis da ta gabata sun hana yan kasuwa da kwastomominsu shiga kasuwar a yayin da gwamnatin jihar ta sassauta dokar kullen a kwanaki biyu cikin kowace mako.

Gwamna Abdullahi Ganduje a makonni biyu da suka shude ya sanar da kasuwannin Yan Kaba da Yan Lemo ne kawai aka bawa damar budewa a ranakun Litinin da Alhamis daga karfe 10 na safe zuwa 4 na yamma.

An kuma bawa wasu manyan kantina damar budewa domin sayar wa alumma kayan masarufi a ranakun biyu a kowanne mako.

An kuma dakatar da yin sallolin Juma'a da zuwa coci a ranakun Lahadi na kimanin sati uku da suka gabata a yunkurin da jihar ke yi na dakile yaduwar annobar ta korona.

Shugaba Muhammadu Buhari ya saka dokar kullen ne a Kano na tsawon sati biyu bayan kullen na kwanaki bakwai da gwamnatin jihar ta fara saka wa da farko.

Sai dai duk da hakan, wasu masu shaguna sun tafi kasuwar ranar Alhamis da ta gabata domin su bude shagunnan amma yan sanda suka fatattake su.

Bisa la'akari da abinda ya faru a baya, yan sandan sun mamaye dukkan kofofin shiga kasuwar domin tabbatar da cewa masu shagunan sun yi biyaya ga dokar ta gwamnati.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel