Sojoji sun kashe yan bindiga 17 a Kaduna – DHQ

Sojoji sun kashe yan bindiga 17 a Kaduna – DHQ

Hedkwatan Tsaro ta Najeriya ta ce dakarun sojojin Operations Thunder Strike da Whirl Punch tare da hadin gwiwan sojojin sama na Operation Gama Aiki sun kashe yan bindiga 17 a karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna.

The Nation ta ruwaito cewa, mai magana da yawun hedkwatan tsaro, Manjo Janar John Enenche ne ya bayyan hakan a ranar Litinin a Abuja.

Enenche ya ce wasu yan bindigan da dama sun tsere da raunikan harsashi a harin hadin gwiwa da aka kai wa wasu da ake zargin yan bindiga ne a mabuyarsu da ke kusa da kauyukan Mashigi Galbi, Damba, Kabarasha a yankin Gwagwada.

Zaratan sojoji sun kashe yan bindiga 17 a Kaduna – DHQ

Zaratan sojoji sun kashe yan bindiga 17 a Kaduna – DHQ. Hoto daga Channels TV
Source: UGC

Ya ce harin na cikin kokarin da rundunar sojojin ke yi ne domin fatattakar yan bindiga da sauran bata gari daga jihar Kaduna.

DUBA WANNAN: Muhimman abubuwa 7 da ba kowa ya sani ba game da sabon Sarkin Bama

A cewarsa, a yayin fatattakar sojojin, an lalata wasu gidaje uku da coci daya a kauyen Kabarasha amma babu farar hula da ya rasa ransa.

Enenche ya bayyana rashin jin dadinsa game da afkuwar lamarin inda ya kara da cewa an kafa kwamitin bincike tare da gwamnatin jihar Kaduna.

Ya kara da cewa an tattara bayanai a kan gidajen da nufin ba su kudaden da za su yi gyara kuma tuni hankulan mutane ya kwanta a kauyukan.

A cewarsa, tsiraran mutanen da suka bar gidajensu domin tsoron yan bindigan za su kawo harin ramuwar gayya duk sun dawo.

Ya ce, "Rundunar Sojojin Najeriya tana ba wa yan Najeriya tabbacin cewa za ta cigaba da aiki tukuru domin ganin an samar da zaman lafiya da tsaro a yankin Arewa maso Yamma.

"Kazalika, tana mika godiyarta da dukkan alumma bisa goyon baya da hadin kai da suke bayarwa, tana kuma shawartar su da suka cigaba da ba wa rundunar bayyanai masu amfani da za su taimaka wurin gano bata gari."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel