Yanzu-yanzu: Ganduje ya tsawaita dokar kulle a Kano

Yanzu-yanzu: Ganduje ya tsawaita dokar kulle a Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da tsawaita dokar kulle a jihar da sati daya a yunkurin ta na cigaba da yaki da annobar COVID-19 da aka fi sani da korona a jihar.

Kwamishinan labarai na jihar, Muhammad Garba, wanda ya fitar da sanarwar ya ce an dauki matakin ne bayan tattaunawa da gwamnatin tarayya da masu da tsaki a fanin lafiya.

Ya ce an dauki matakin ne domin rage yaduwar cutar tsakanin mutane ta hanyar cudanya wadda ke daya daga cikin hanyar da cutar ke yaduwa kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Sanarwar ta yi kira ga alummar jihar su kara hakuri tare da ba wa gwamnati goyon bayan a yakin da ta ke yi da annobar duk da irin halin da mutane ke ciki.

Yanzu-yanzu: Ganduje ya tsawaita dokar kulle a Kano

Yanzu-yanzu: Ganduje ya tsawaita dokar kulle a Kano. Hoto daga Sani Maikatanga
Source: Twitter

Ta kuma yi kira ga mutane su cigaba da tsafta ta hanyar yawaita wanke hannun su da sabulu, saka takunkumin fuska da kauracewa taron jama'a.

DUBA WANNAN: Karkatar da tallafin COVID-19: An kama shugaban karamar hukuma a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa kotun tafi da gidanka a jihar Kano na hukunta wadanda suka saba dokar kulle da aka kafa sakamakon bullar COVID-19 ta zartar da hukunci a kan wasu limamai biyu da aka samu da laifin saba dokar.

An yanke wa limaman biyu hukuncin share gidan hakimi har na tsawon kwanaki bakwai kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Baba Jibo Ibrahim, Cif Rajistara na jihar Kano ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Jumaa 9 ga watan Mayu.

A cewarsa, lamarin ya faru ne a karamar hukumar Minjibir na jihar.

Kotun ta yanke hukuncin cewa limamen su rika share gidan hakimin Minjibir na tsawon sati daya baya da tarar Naira 10,000.

Ya kara da cewa a lokacin da suke gudanar da wannan aikin, jamian karamar hukumar za su rika zuwa suna duba su domin tabbatar da cewa sun aikata aikin yadda ya dace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel