Korona: Ta harbi karin mutum 242 a Najeriya, 64 a Kano, 49 a Katsina, 13 a Kaduna

Korona: Ta harbi karin mutum 242 a Najeriya, 64 a Kano, 49 a Katsina, 13 a Kaduna

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa a Kasa (NCDC) ta ce annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 381 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 11:45 na daren ranar Talata, 11 ga watan Mayun na shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa karin sabbin mutane 242 din sun fito daga jihohin Najeriya kamar haka;

88-Lagos

64-Kano

49-Katsina

13-Kaduna

9-Ogun

6-Gombe

4-Adamawa

3-FCT

1-Ondo

1-Oyo

1–Rivers

1-Zamfara

1-Borno

1-Bauchi

DUBA WANNAN: Muhimman abubuwa 7 da ba kowa ya sani ba game da sabon Sarkin Bama

NCDC ta ce ya zuwa karfe 11:45 na daren ranar Talata, 12 ga watan Mayu, akwai jimillar mutane 4641 da aka tabbatar da cewa suna dauke da kwayar cutar Covid-19 a fadin Najeriya.

An sallami mutane 902 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 150.

A wani labarin, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ce daga yanzu saka takunkumin fuska ya zama wajibi a Kano tare da bayyana cewa za a gurfanar da wadanda aka samu suna saba doka.

Ganduje ya bayyana hakan ne ranar Lahadi yayin da yake gabatar da jawabi a kan halin da jihar Kano ke ciki dangane da annobar korona.

Gwamnan Ganduje ya bayyana cewa gwamnatinsa ta kafa kotun tafi da gidanka guda 10 domin hukunta masu karya dokar kulle tare da bayyana cewa an saka dokar ne domin dakile yaduwar annobar a jihar.

A cewar gwamna Ganduje, gwamnati za ta samar da takunkumin fuska ga jama'a kyauta.

Kazalika, ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta hada kai da telolin cikin gida domin samar da isassun taunkumi ga jama'a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel