Buhari ya bamu umurnin karbo maganin Koronan kasar Madagascar - SGF, Boss Mustapha

Buhari ya bamu umurnin karbo maganin Koronan kasar Madagascar - SGF, Boss Mustapha

Shugaba Muhammadu Buhari ya umurci kwamitin kar ta kwanan fadar shugababan kasa na yaki da cutar COVID-19 da su hanzarta karbo maganin Koronan da kasa Madagascar ta hada.

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, wanda shine shugaban kwamitin ya bayyana hakan ne ranar Litinin a hirar da kwamitin tayi da manema labarai kamar yadda ta saba.

Ya ce kasar Madagascar ta baiwa Najeriya gudunmuwar maganin ta kasar Guinea Bissau kuma ana shirye-shiryen karbosu.

Mustapha ya ce shugaban kasa ya kara da cewa sai an gwada maganin kafin a fara baiwa mutane.

Buhari ya yi umurni mu karbo maganin Koronan kasar Madagascar - SGF, Boss Mustapha

CVO organic
Source: Twitter

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Karin mutane 33 sun warke daga Coronavirus, an sallamesu

Da safe mun kawo muku rahoton cewa Jamhuriyar Madagascar ta bukaci aiko da maganin gargajiyar da take amfani da shi wajen yaki da cutar coronavirus ga Najeriya da sauran kasashen nahiyar Afrika.

Kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa, ana amfani da maganin wajen kariya da kuma maganin cutar.

Wakilan Najeriya sun garzaya kasar Equatorial Guinea inda za a karbo maganin tare da dauko shi zuwa Abuja.

Don saukake al'amarin sufuri, a raba kasashen Afrika zuwa yankuna inda Najeriya ta fada yankin Equatorial Guinea.

A daren jiya Lahadi ne Najeriya ta tabbatar da kamuwar mutum 4,399 da muguwar cutar, kamar yadda hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa (NCDC) ta bayyana.

Za ku tuna cewa hukumar lafiya ta duniya W.H.O dake jagorantar yaki da COVID ta nuna rashin amincewarta da maganin na Madagascar inda tace kawai maganin gargajiya ne ba na Coronavirus ba.

Hakan bai yiwa yan nahiyar Afrika dadi ba inda alkaluma suka ce kawai ana kokarin watsi da maganin ne saboda bakin fata ya hada.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel