Yanzu-yanzu: Karin mutane 33 sun warke daga Coronavirus, an sallamesu

Yanzu-yanzu: Karin mutane 33 sun warke daga Coronavirus, an sallamesu

An samu karin mutane 33 da suka samu waraka daga muguwar cutar Coronavirus a jihar Legas ranar Litinin, 11 ga Mayu, 2020, gwamnatin jihar ta bayyana.

Ma'aikatar lafiyan jihar ta bayyana hakan ne a shafinta na Tuwita inda tace:

"Masu cutar COVID-19 a Legas 33; mata 9 da maza 24; dukka yan Najeriya sun shaqi kamshin yanci daga cibiyoyin killace Onikan da Eti-Osa kuma tuni sun koma wajen iyalansu."

Marasa lafiyan, 17 daga Onikan, da 16 daga Eti-osa sun warke gaba daya daga cutar bayan gwaji biyu sun nuna cewa sun barranta daga COVID-9."

"Kawo yanzu, adadin wadanda akayi jinya kuma aka sallama a Legas ya kai 502."

KU KARANTA: Buhari ya bamu umurnin karbo maganin Koronan kasar Madagascar - SGF, Boss Mustapha

A daren jiya Lahadi ne Najeriya ta tabbatar da kamuwar mutum 4,399 da muguwar cutar, kamar yadda hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa (NCDC) ta bayyana.

An samu sabbin karin masu cutar 81 a jihar Legas, jihar Jigawa ke biye mata baya da mutum 35 sai Borno da ke da 26.

Jihar Kano ta tabbatar da kamuwar karin mutum 26, jihar Bauchi ce mai mutum 20.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel