Masu sukar mu da yi wa dokar hana fita sakwa-sakwa ba su san komai ba a kan Kano - Ganduje

Masu sukar mu da yi wa dokar hana fita sakwa-sakwa ba su san komai ba a kan Kano - Ganduje

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje, ya bayyana cewa masu suka gami da hayaniya saboda an sassauta dokar hana fita a jihar ba su san komai ba game da jihar.

Ganduje ya ce masu caccakar gwamnatinsa saboda ta yi wa dokar hana fita sakwa-sakwa a jihar surutu kawai suke amma sun jahilci menene jihar Kano.

Ana ci gaba da bayyana damuwa kan yiwuwar ci gaba da yaduwar cutar korona muddin aka sassauta dokar hana fita kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

Sai dai a yayin taron fara rarrabi takunkumin rufe fuska a jihar a ranar Litinin, Ganduje ya ce wadannan masu hayaniyar suna zaune ne kawai cikin ofis suna shan sanyin na'ura mai sanyaya daki a birnin Abuja, amma babu abin da suka sani game da jihar.

"Wadanda ke sukar matakan da gwamnatin Kano ta shimfida wajen sassauta dokar hana fita, suna zaune ne a ofisoshinsu suna shakar iska ta na'ura mai sanyaya daki a Abuja kawai, amma sun jahilci ko mecece jihar Kano."

Gwamnan Kano; Abdullahi Ganduje sanye da takunkumin rufe fuska
Gwamnan Kano; Abdullahi Ganduje sanye da takunkumin rufe fuska
Asali: UGC

"Suna yin hayaniya ne kawai saboda ba su san komai ba game da Kano, babu abin da suka fahimta game da yanayin ganuwar zamantakewa ta jihar" inji gwamnan.

"Kano babban birni ne mai dimbin jama'a da ya dara mafi akasarin jihohin kasar nan ta kowace irin siga. Yana kamanceceniya da manyan birane na kasashen duniya da ya zama dole a ba shi kulawa ta musamman."

KARANTA KUMA: Coronavirus: Babu ranar komawar dalibai makarantu tukunna – Gwamnatin Tarayya

Ganduje wanda ake yiwa lakabi da Khadimul Islama, ya ce kwamishinoninsa zai dora wa nauyin rarraba takunkuman rufe fuska a yunkurin da gwamnatinsa ta ke yi na dakile yaduwar cutar korona.

Gwamnan ya kara da cewa, za a sassautawa 'yan kasuwar mayanka su rika cin kasuwa a ranakun Litinin da Alhamis, domin kauce wa yadda suke yanka dabbobi a kowane lungu da sako suka samu na cikin birni.

Wannan furuci na gwamnan Kano ya zo ne bayan kwana guda da yiwa takwaransa na Kaduna, Mallam Nasir El Rufa'i, martani a kan siyasantar da lamarin almajirai da ake mayar da su mahaifarsu domin dakile yaduwar cutar.

Legit.ng ta ruwaito cewa, Ganduje ya ya yiwa al'ummar Kano sassauci a kan dokar hana kulle, inda ya basu damar fita domin cefanen abinci a ranakun Litinin da Alhamis na kowane mako.

Ana iya tuna cewa, makonni biyu da suka gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zartar da dokar kulle a kan jihar Kano, sanadiyar yadda likafar annobar korona ta ke ci gaba tamkar wutar daji babu sassauci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel