Coronavirus: Babu ranar komawar dalibai makarantu tukunna – Gwamnatin Tarayya

Coronavirus: Babu ranar komawar dalibai makarantu tukunna – Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayya ta bukaci 'yan Najeriya da su yi watsi da jita-jitar da ake yadawa kan batun ranar komawa makarantu.

Rahoton da jaridar Daily Nigerian ta ruwaito, gwamnatin ta yi gargadin cewa dukkanin makarantu da ke fadin kasar za su ci gaba da kasancewa a rufe.

Gwamnatin ta bayyana wa iyayen dalibai da kuma daliban kansu da su yi watsi da duk wani rade-radin da ake yadawa kan ranar komawa makarantu.

Idan ba a manta ba, biyo bayan barkewar annobar korona a Najeriya, gwamnatin tarayya cikin gaggawa ta ba da umarnin rufe duk wasu makarantu a fadin kasar.

Baya ga umarnin rufe makarantu, gwamnatin tun a watan Maris ta kuma sanya dokar hana fita kasuwanni da sauran tarurrukan jama'a da na addini a yunkurin dakile yaduwar cutar a duk fadin kasar.

Ministan Ilimi; Adamu Adamu
Ministan Ilimi; Adamu Adamu
Asali: UGC

Ministan ilimi, Adamu Adamu, shi ne ya yi wannan karin haske cikin wata sanarwa mai lamba FME/PSE/HE/1041/C 1/Vol.1/137 da sakataren dindindin na ma'aikatarsa, Sonny Echono ya sanya wa hannu.

Sanarwar da ma'aikatar ilimin kasar ta fitar ta nemi al'ummar kasar da sauran masu ruwa da tsaki da su yi kaffa-kaffa da labarai na boge musamman a wannan yanayi da ake ciki.

KARANTA KUMA: Akwai yiwuwar za a rage yawan ma'aikatan gwamnati a Najeriya - NASU

Mista Echono ya ce har kawo yanzu ba a sanya ranar da dalibai za su koma makaranta ba, lamarin da ya a madadin haka ake shawartar al'umma da su ci gaba da daukar matakan da suka wajaba domin kauce wa kamuwa ko da cutar korona.

Cikin sanarwar da ma'aikatar ilimin ta fitar zuwa dukkanin hukumomin ilimi na kasar, ta nemi daliban makarantu a kowane mataki da su yi zaman dirshan a gida har sai an ga abin da hali ya yi game da annobar korona.

A wani rahoton mai nasaba da wannan, cutar korona ta harbi akalla ma'aikatan lafiya 47 a jihar Kano kamar yadda gwamnatin jihar ta bayyana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel