Akwai yiwuwar za a rage yawan ma'aikatan gwamnati a Najeriya - NASU

Akwai yiwuwar za a rage yawan ma'aikatan gwamnati a Najeriya - NASU

Kungiyar ma'aikatan da ba sa koyarwa a cibiyoyin ilimi NASU, ta bayyana damuwa game da shawarar da gwamnatin tarayya ke neman dauka wadda za ta yi sanadiyar rage yawan ma'aikatan gwamnati a kasar.

Ana iya tuna cewa, a shekarar 2011 ne tsohuwar gwamnatin shugaban kasa Goodluck Jonathan, ta kafa wani kwamitin binciken a kan yadda za a sauya fasali da takaice ma'aikatun gwamnatin Najeriya.

Bayan fitowar sakamakon binciken a shekarar 2012, tsohuwar gwamnatin ta yiwa sakamakon binciken lakabi da 'Oransaye Report 2012', da ya biyo daga sunan wanda ya jagoranci kwamitin, tsohon shugaban ma'aikata, Mista Steve Oransaye.

A yanzu gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta ba da umarni a ci gajiyar wannan bincike na takaice ma'aikatun gwamnatin tarayya a kasar gami da sauya masu fasali.

Kungiyar NASU cikin wata sanarwa da fitar a ranar Lahadi da sa hannun sakataren ta, Peters Adeyemi, ta yi gargadin cewa amfani da wancan sakamako zai janyo ma'aikatan gwamnati da dama za su rasa aikinsu.

Kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito, kungiyar ta kuma ce hakan zai janyo fitina ta yadda kangi na talauci zai yi wa kasar katutu.

Bugu da kari NASU ta ce ma'aikatun gwamnatin da ake neman sauya fasali da takaicewa, sun samo tushe ne daga dokoki da kuma kundin tsarin mulki na kasa da ya ba da lasisin kirkirarsu tun fil azal.

Ministar kudin kasar, Zainab Ahmed da shugaba Muhammadu Buhari

Ministar kudin kasar, Zainab Ahmed da shugaba Muhammadu Buhari
Source: UGC

Kungiyar ta lura cewa muddin za a sauya fasali da takaice wasu ma'aikatu, dole ne sai an sake dogon waiwaye a kan dokokin kasar gami da yi wa kundin tsarin mulkin na kasa kwaskwarima kafin hakan ta tabbata.

"Akwai karancin manufofi a Najeriya wanda za su taimaka wajen kawar da rashin aikin yi. Saboda haka ba za a yarda gwamnati ta yi amfani da duk wani tsari da zai janyo barazana ga ma'aikata ba a kasar tare da jefa su cikin talauci."

KARANTA KUMA: Gwamnatin Bauchi ta kayyade farashin kayan abinci

A baya bayan nan shugaba ne Buhari ya amince a kan a aiwatar da sakamakon binciken kwamitin Steve Oransaye, dangane da takaice ma'aikatu da cibiyoyin gwamnati a kasar.

Ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren kasa, Zainab Shamsuna Ahmed, ita ce ta bayyana hakan yayin wani shiri kan siyasa mai taken Politics Today, wanda kamfanin sadarwa na Channels TV ke daukar nauyi.

Gwamnatin tsohon shugaban kasa ta kafa kwamitin ne a wancan lokaci da manufar rage farashin tafiyar da al'amuran gwamnati a Najeriya, sanadiyar yadda ya dara na sauran kasashen duniya tsada.

Kwamitin ya ba da shawarar a rage yawan hukumomin gwamnati daga 263 zuwa 161.

Bayan samun amincewar shugaban Buhari, ministar kudin kasar ta ce tuni an fara bijiro da hanyoyin rage wannan tsada ta tafiyar da sha'anin gwamnati da jagoranci, ta hanyar amfani da sakamakon binciken da kwamitin Steve Oransaye ya gudanar a 2012.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel