Gwamnatin Bauchi ta kayyade farashin kayan abinci

Gwamnatin Bauchi ta kayyade farashin kayan abinci

A yayin da farashin kayan masarufi suka yi tashin doron zabuwa a Najeriya musamman tun a lokacin da watan Azumi ya rage sauran 'yan kwanaki, mun ji cewa a yanzu gwamnatin Bauchi ta yi abun a yaba mata.

Duba da hauhawar farashin kayan masarufi, gwamnatin jihar Bauchi ta kayyade farashin wasu nau'ikan kayayyakin abinci domin saukakawa al'ummarta musamman a wannan yanayi da ake ciki.

Wannan sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar a ranar Lahadi, 10 ga watan Mayu, ta na kunshe ne cikin wani sako mai dauke da sa hannun hadimin gwamnan a kan sadarwa, Mukhtar Gidado.

Biyo bayan wata ganawa da wakilan 'yan kasuwa da kuma kwamitin kula da gwamnatin jihar ta kafa kan cutar korona, sun yanke shawarar rage farashin wasu kayayyakin abinci domin samun falalar watan Azumin Ramadana.

Gwamnan jihar Bauchi; Sanata Bala Muhammad
Gwamnan jihar Bauchi; Sanata Bala Muhammad
Asali: Twitter

Babu shakka watan azumi lokaci ne da mutane ke da mafificiyar bukata ta kayan abinci, sai dai kuma rashin abin hannu ya sa mutane da dama su na cikin halin ni 'ya su, sanadiyar annobar korona da ta hana fita neman na abincin.

Gwamnatin jihar ta yaba da wannan hobbasa da kuma hadin kan da ta samu daga bangaren wakilan 'yan kasuwan, lamarin da ta ce rage farashin kayan abinci musamman a wannan lokaci zai rage radadin da al'umma ke fuskanta.

KARANTA KUMA: Yawan mace-mace ya jefa masu hakar kabari cikin firgici a Kano

A yayin haka kuma gwamnan jihar, Sanata Bala Muhammad, ya shawarci al'ummar jihar da su ci gaba da bin ka'idojin gwamnati gami da kuma daukan matakan kare kai bisa ga tanadin da mahukuntan lafiya suka yi.

Ga sabon farashin jerin kayayyakin abincin da 'yan kasuwa suka rangwanta wa al'umma a Bauchi:

1. Buhun shinkafa - Daga N18, 000 zuwa N17, 500

2. Buhun Sukari - Daga N22, 000 zuwa N17, 000

3. Buhun Gero - Daga N12, 500 zuwa N12, 000

4. Jarkar Man ja - Daga N9, 500 zuwa N9, 000

5. Kilo daya na Naman miya - Daga N1, 250 zuwa N1, 200.

Gwamnatin ta nemi a rage farashin kayayyakin ne bayan la'akarin da ta yi a kan halin tsanani da al'umma ke ciki sanadiyar yadda annobar korona ta dagula al'amura tare da hana ruwa gudu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel