Bala Muhammad ya rufe kananan hukumomi 3 a jahar Bauchi saboda Coronavirus

Bala Muhammad ya rufe kananan hukumomi 3 a jahar Bauchi saboda Coronavirus

Gwamnan jahar Bauchi, Sanata Bala Muhammad Kauran Bauchi ya sanar da garkame wasu kananan hukumomi guda uku a jahar Bauchi sakamakon bullar annobar Coronavirus.

Daily Trust ta ruwaito gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Lahadi, 10 ga watan Mayu na shekarar 2020 inda yace ya rufe garuruwan Katagum, Giade da kuma Zaki.

KU KARANTA: An sallami mutumin da ya fara kai cutar Coronavirus jahar Kano, da wasu 9

Bala ya danganta wannan mataki da ya dauka ga rahotannin da aka samu na mace mace a kananan hukumomin da kuma yaduwar cutar Coronavirus a cikinsu.

Bala Muhammad ya rufe kananan hukumomi 3 a jahar Bauchi saboda Coronavirus
Bala Muhammad Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

A dalilin yaduwar cutar da aka samu a kananan hukumomin Zaki, Giade da Katagum, adadin masu cutar Coronavirus a jahar Bauchi ya yi tashin gwauron zabi zuwa 181.

Don haka gwamnan ya bayyana cewa dole ne ta sa suka dauki wannan matakin garkame garuruwan na tsawon kwanaki 10 domin dakatar da yaduwar cutar a cikin al’umma.

“Dole mu rufe kananan hukumomin guda uku, yanzu muka samu sakamakon mutane 66 da suka kamu da cutar, 42 daga cikinsu mutanen Azare ne, mun gano a Azare cutar ta yi kamari a tsakanin jama’a.

“Jama’a basu dabbaka matakin kariya da aka gindaya saboda suna ta gudanar da hada hadarsu a tsakanin Azare zuwa jahar Kano, jahar dake da matsalar annobar sosai.” Inji shi.

Gwamnan ya umarci mataimakinsa, Baba Tela ya koma ya tare a yankin Katagum domin sa ido a kan yadda za’a gudanar da aikin bin diddigin duk wadanda suka yi mu’amala da masu cutar.

Haka gwamnan ya umarci Tela ya kula da yadda ake gudanar da gwajin mutane domin gwamnatin jahar ta samu takamaimen adadin wadanda suka kamu da cutar.

“Da gaske muke wannan lamarin, shi yasa na umarci mataimakin gwamna ya koma Katagum, yayin da ni kuma zan kula da tsakiya, na tattauna da kwamishinan Yansanda don ya tabbatar da an garkame ko ina.”

Haka zalika ya umarci kwamitin rabon kayan tallafi su tabbata jama’an yankunan uku sun samu tallafin kayan abinci domin rage musu radadin dokar ta bacin.

Daga karshe ya yi alkawarin yin feshi a garuruwan, ya kuma roki cibiyar gwaji dake Vom a garin Jos su taimaka ma Bauchi da yi musu gwaje gwaje a cikin lokaci kafin su kammala nasu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel