Baturiya da ta taso daga kasar Amurka don ganin saurayinta a Najeriya ta mutu a Otal

Baturiya da ta taso daga kasar Amurka don ganin saurayinta a Najeriya ta mutu a Otal

Rai bakon duniya, wata baturiya yar shekarar 60 daga kasar Amurka ta rasu a wani Otal dake Warri bayan ta kawo ma saurayinta ziyara a jahar Delta.

Mai karatu, ba’a yi kuskure ba idan aka ce wannan baturiya ta kira ma saurayinta ruwa, saboda a yanzu haka yana can ido ya raina fata a hannun rundunar Yansandan jahar Delta.

KU KARANTA: An sallami mutumin da ya fara kai cutar Coronavirus jahar Kano, da wasu 9

Kamfanin dillancin labarun Najeriya ta ruwaito matar ta mutu ne bayan da wasu alamu dake nuna ta kamu da annobar cutar Coronavirus mai sarke numfashin mutum.

Baturiya da ta taso daga kasar Amurka don ganin saurayinta a Najeriya ta mutu a Otal
Saurayin Hoto: Shafin Sahara Reporters
Asali: Facebook

Kwamishinan Yansandan jahar Delta, Hafiz Inuwa ya tabbatar da mutuwar baturiyar a garin Warri a ranar Lahadi, 10 ga watan Mayu na shekarar 2020.

“Bayan ta kawo ma saurayin nata ziyara, sai ya ajiye ta a wani Otal tsawon mako 1, daga nan ya dauke ta zuwa wani Otal a Orerokpe, suna tare tsawon mako daya sai ta fara fama da tari, yawo bayan gida da kuma sarkewar numfashi.

“Daga nan sai aka garzaya da ita asibiti bayan jikin nata ya tsananta, a can ta rasu. A yanzu haka muna tsare da saurayin nata a ofishin Yansanda dake Orerokpe.” Inji shi.

Baturiya da ta taso daga kasar Amurka don ganin saurayinta a Najeriya ta mutu a Otal
Gawar Hoto: Sahara Reporters
Asali: Facebook

Kwamishinan ya kara da cewa ya sanar da kwamishinan kiwon lafiya na jahar Delta domin su nemi jami’an hukumar NCDC dangane da alamun da suka gani tattare da matar.

Sa’annan ya gargadi jami’an Yansanda da su bi a hankali wajen yadda zasu yi mu’amala da matashin saurayin, don gudun kada su kamu da cutar COVID-19.

A wani labari kuma, Allah da ikon sa, mutumin da ya fara kamuwa da cutar Coronavirus a jahar Kano, Ambassada Kabiru Rabiu ya warke sarai daga mugunyar cutar mai toshe numfashi.

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito shugaban kwamitin yaki da cutar Coronavirus ta jahar Kano, Tijjani Hussaini ne ya tabbatar da haka, inda yace tuni an sallami Kabiru.

Tijjani ya ce an sallami Kabiru ne bayan an sake gudanar da gwajin cutar a kansa har sau biyu, kuma aka yi sa’a sakamakon gwajin ya nuna cewa baya dauke da cutar kuma.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel