An sallami mutumin da ya fara kai cutar Coronavirus jahar Kano, da wasu 9

An sallami mutumin da ya fara kai cutar Coronavirus jahar Kano, da wasu 9

Allah da ikon sa, mutumin da ya fara kamuwa da cutar Coronavirus a jahar Kano, Ambassada Kabiru Rabiu ya warke sarai daga mugunyar cutar mai toshe numfashi.

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito shugaban kwamitin yaki da cutar Coronavirus ta jahar Kano, Tijjani Hussaini ne ya tabbatar da haka, inda yace tuni an sallami Kabiru.

KU KARANTA: An samu bullar annobar COVID-19 a yankunan karkara – Gwamna El-Rufai

Tijjani ya ce an sallami Kabiru ne bayan an sake gudanar da gwajin cutar a kansa har sau biyu, kuma aka yi sa’a sakamakon gwajin ya nuna cewa baya dauke da cutar kuma.

An sallami mutumin da ya fara kai cutar Coronavirus jahar Kano, da wasu 9
Kabiru Hoto: The Nigerian Voice
Asali: UGC

Idan za’a tuna a ranar 11 ga watan Afrilu ne aka gano Kabiru yana dauke da cutar bayan ya tafi wani asibiti mai zaman kansa dake unguwar Nassarawa GRA domin a duba lafiyarsa.

Daga bisani jami’an hukumar kare yaduwar cututtuka, NCDC suka cimma sa a asibitin sakamakon nemansa da suke ta yi saboda kafin nan ya basu samfurin sa don a su gwada shi.

Malam Hussaini ya bayyana cewa a ranar Lahadi aka sallami Kabiru daga cibiyar killace masu cutar dake Kwanar Dawaki.

A hannu guda kuma, gwamnatin jahar Kano ta bayyana cewa ta sallami mutane 10 daga cibiyoyin killace masu cutar Coronavirus a jahar bayan sun warke daga muguwar cutar.

Kwamishinan watsa labaru na jahar, Malam Muhammad Garba ne ya bayyana haka a ranar Lahadi, inda yace hakan ya kawo adadin mutanen da suka warke a jahar zuwa 32.

Garba yace kafin a sallami mutanen, sai da aka tabbatar da sakamakon gwajin da aka musu sau biyu sun nuna sun rabu da cutar, sa’annan aka mika su ga iyalansu.

Garba ya kara da cewa an samu mutane 3 da suka mutu, wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu zuwa 21. Zuwa yanzu jahar Kano ta yi ma mutane 2,972 gwaji a cibiyoyinta dake jahar.

Daga karshe kwamishinan ya shawarci jama’an jahar su kasance masu biyayya ga matakan kariya da gwamnatin jahar ta gindaya don kare kansu daga cutar COVID-19.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel