Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un: Dan majalisar dokokin jahar Katsina ya rasu

Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un: Dan majalisar dokokin jahar Katsina ya rasu

Wani dan majalisa dake wakiltar mazabar karamar hukumar Bakori a jahar Katsina, Abulrazak Ismaila Tsiga ya rigamu gidan gaskiya.

Takwaransa, dan majalisa mai wakiltar mazabar Safana, Abduljalal Haruna Runka ne ya bayyana haka a shafinsa na dandalin sadarwar zamani na Facebook a daren Lahadi.

KU KARANTA: An samu bullar annobar COVID-19 a yankunan karkara – Gwamna El-Rufai

“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun, allah yayima Hon Abdulrazak Ismail Tsiga Rasuwa yanzu ( Danmajalisar Bakori), zaayi jana'izar shi gobe idan Allah ya kaimu a garin Tsiga, Allah ya mashi rahama amin” inji shi.

Rahotanni sun bayyana dan majalisa Abdulrazak ya rasu ne da yammacin Lahadin a babban asibitin garin Malumfashi bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya.

Sai dai wasu majiyoyi sun bayyana cewa dan majalisar ya dade yana fama da matsananciyar rashin lafiya, tun bayan da aka rantsar da su a majalisar a ranar 6 ga watan Yuni.

A wani labarin kuma, kwamishinan filaye da gidaje na jahar Sakkwato, Surajo Marafa Gatawa ya rasu a ranar Lahadi bayan fama da yayi da gajeruwar rashin lafiya.

Gwamnan jahar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da hadiminsa a bangaren watsa labaru, Muhammad Bello ya fitar.

An haifi Gatawa ne a ranar 15 ga watan Satumbar 1957, ya taba zama kansila a karamar hukumar Sabon Birni daga 1988-1989, ya zama shugaban karamar hukumar daga 1991-1993.

Daga bisani ya zama dan majalisar tarayya daga 1999-2007, sa’annan ya zama kwamishina a gwamnatin Tambuwal tun daga shekarar 2015. Ya rasu ya bar mata uku da yara da dama.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Online view pixel