Karkatar da tallafin COVID-19: An kama shugaban karamar hukuma a Kano

Karkatar da tallafin COVID-19: An kama shugaban karamar hukuma a Kano

- Hukumar sauraron korafin jama'a da yaki da rashawa ta jihar Kano ta kama shugaban karamar hukumar Panshekara

- An kama Alhaji Kabiru Ado Panshekara ne bisa zarginsa da karkatar da kayan tallafin korona a karamar hukumarsa

- Hukumar yaki da rashawar ta ce Ado Panshekara ya raba wa wasu rukunin jami'an tsaro kayan tallafin a maimakon talakawa wadda hakan ya saba doka

Hukumar sauraron korafin alumma da yaki da rashawa na jihar Kano ta kama Shugaban karamar hukumar Kumbotso, Alhaji Kabiru Ado Panshekara a kan zarginsa da amfani da kujerarsa ba bisa kaida ba wurin rabon kayan tallafin da gwamnati ta bayar sobada kullen korona.

Shugaban Hukumar, Muhuyi Magaji Rimigado ya tabbatar da kama shugaban karamar hukumar a ranar Asabar kamar yadda New Telegrah ta ruwaito.

Karkatar da tallafin COVID-19: An kama shugaban karamar hukuma a Kano

Karkatar da tallafin COVID-19: An kama shugaban karamar hukuma a Kano. Hoto daga NLC
Source: UGC

DUBA WANNAN: COVID-19: Korona ta kashe wani fitaccen Dan Kasuwa a Yobe

Ya ce Alhaji Panshekara ya saba dokar Hukumar sauraron korafin alumma da yaki da rashawa na jihar Kano na shekarar 2008 a yayin rabon kayan tallafi da gwamnati ta bayar a karamar hukumarsa.

Hukumar ta ce shugaban na karamar hukumar Kumbotso ya bawa jami'an tsaro da suka hada da yan sanda, jami'an hukumar yan sandan farar hula, DSS, da jami'an hukumar Hisbah wadda hakan ya saba wa sashi na 22, 23 da 26 na dokar Hukumar sauraron korafin al'umma da yaki da rashawa na jihar Kano na shekarar 2008.

A wani labarin, kun ji cewa Allah ya yi wa mai bawa Gwamna Muhammadu Badaru shawara na musamman akan harkokin ilimin manya da na manyan makarantu, Ibrahim Ismail, rasuwa.

Marigayi Jarman Ringim kuma tsohon shugaban hukumar cigaban kananan hukumomi ya rasu ne a ranar Jumaa bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Sanarwar rasuwar ta fito ne daga bakin babban mataimaki na musamman ga maigirma Gwamnan Jihar Jigawa a sabbin kafafan sadarwa, Auwalu D. Sankara a shafinsa na Facebook.

Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ya yi ta’aziyya ga daukacin al’ummar da ke masarautar Ringim bisa rasuwar Alhaji Ibrahim Ismail Jarman Ringim wanda ya rasu ranar Jumaa bayan fama da rashin lafiya da ya yi.

Alhaji Badaru da karshe yayi addua ga Allah subhanahu wata’ala da ya saka wa mamacin da aljanna firdausi kuma ya bai wa iyalan sa karfin gwiwar juriya da rashin da su kayi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel