Tsaro: Gwamna Zulum ya bude sabon ofis a Auno

Tsaro: Gwamna Zulum ya bude sabon ofis a Auno

Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno zai kafa ofishi a kauyen Auno da ke karamar hukumar Konduga na jiharsa domin karfafa wa mutanen kauyen gwiwa da suka gudu saboda tsoron yan ta'adda su dawo gida.

A yayin da ya kai ziyara kauyen a ranar Asabar, Zulum ya ce zai rika amfani da ofishin daga lokaci zuwa lokaci domin karfafawa mutanen kauyen gwiwa su dawo gida.

Ya ce hakan na da muhimmanci sosai duba da kusancin da Auno ke da shi da babban birnin jihar da kuma Jami'ar jihar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnan ya bukaci a kara samar da jamian tsaro a kauyen domin hakan zai karfafa wa mutane gwiwa.

Tsaro: Gwamna Zulum ya bude sabon ofishi a Auno
Tsaro: Gwamna Zulum ya bude sabon ofishi a Auno. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Dokar kulle: Limamai za su share gidan hakimi na sati daya a Kano

Ya kuma umurci Ma'aikatar Sake Gina Garuruwa ta Tallafawa wadanda Iftilai ya fada musu ta yi gaggawar samar da abinci da kudi ga wadanda suke zaune a garin a halin yanzu.

Zulum ya ce, "Kamar yadda na fada a baya, Auno gari ne mai muhimmanci kuma saboda kallubalen tsaro a Auno, mafi yawancin mutanen garin sun koma Maiduguri.

"Nisan kilomita shida kawai daga Jamiar Jihar Borno zuwa Auno, korar mutane daga Auno yana nufin korar yan Maiduguri kuma rabin mutanen jihar suna Maiduguri ne.

"Ya zama dole mu dauki matakin kare Auno kamar sauran garurruwan jihar. Zan kafa wata shirin samar da gidaje domin idan na zo gari nima in samu wurin sauka.

"A yayin da muke yaki da COVID-19, ya zama dole mu kula sosai da sauran bangarorin rayuwa. Auno garin manoma ne kuma damina ne yanzu, ya kamata mutane su koma gona.

"Mafi yawancin mutanen Maiduguri suna noma a Auno. Don haka yana da muhimmanci mu mayar da hankali wurin samar da tsaro a Auno."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel