Shagalin bikin nadin sarautar sabon Sarkin Bama (Hotuna)

Shagalin bikin nadin sarautar sabon Sarkin Bama (Hotuna)

Bayan rasuwar Shehun Bama, Alhaji Kyari El-Kanemi, Gwamna Babagana Zulum ya nada sabon sarki a Bama.

Amma a yau Asabar, 9 ga watan Mayun 2020 aka yi bikin nadin sarautar sabon sarkin Alhaji Umar Ibn Kyari El-Kanemi.

Shagalin bikin nadin sarautar sabon Sarkin Bama (Hotuna)

Shagalin bikin nadin sarautar sabon Sarkin Bama (Hotuna).. Hoto daga TVC News
Source: Twitter

Kamar yadda Legit.ng ta wallafa, Alhaji Umar Ibn Kyari Al Amin El-Kanemi, babban dan marigayi Shehun Bama, Alhaji Kyari Ibn Umar Al Amin Ibn Ibrahim El Kanemi, ya zama sabon Shehun masarautar Bama.

Tawagar gwamnatin jihar Borno karkashin jagorancin Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Usman Jidda Shuwa, suka gabatar da wasikar ga sabon sarkin masarautar a ranar Litinin, 4 ga watan mayu, 2020.

Sauran mambobin tawagar sun hada da kwamishinan harkokin kananan hukumomi da masarautun gargajiya da Daraktan lamuran masarautu.

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya nada shi ne da sharadin cewa zai zauna a garin Bama ba ya rika mulkan al'ummarsa daga Maiduguri ba.

Shagalin bikin nadin sarautar sabon Sarkin Bama (Hotuna)

Shagalin bikin nadin sarautar sabon Sarkin Bama (Hotuna). Hoto daga TVC News
Source: Twitter

KU KARANTA: Shekau ya samu taimakon Euro miliyan 5 daga wata kungiya: Gaskiya ta al'amari ya bayyana

Shagalin bikin nadin sarautar sabon Sarkin Bama (Hotuna)

Shagalin bikin nadin sarautar sabon Sarkin Bama (Hotuna). Hoto daga TVC News
Source: Twitter

Sakataren gwamnatin jihar yace: "Mai girma (gwamna) ya umurceni da fada maka cewa ka zauna a Bama saboda ya nunawa jama'arka kana tare da su."

Shagalin bikin nadin sarautar sabon Sarkin Bama (Hotuna)

Shagalin bikin nadin sarautar sabon Sarkin Bama (Hotuna). Hoto daga TVC News
Source: Twitter

A wani labari na daban, Sabon Shehun Bama, Shehu Umar II El-Kanemi, ya kai wa gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ziyara ta ban girma domin yin mubaya a bayan nada shi sarauta.

Gwamna Zulum ya nada Shehu Umar II ne a matsayin sabon Shehun Bama a ranar 4 ga watan Mayun 2020 bayan rasuwar mahaifinsa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A yayin da ya ke tarbar sarkin a gidan gwamnati a Maiduguri a ranar Laraba, Gwamna Zulum ya mika godiyarsa ga Shehun saboda ziyarar ya kuma zaburar da shi bisa babban aikin da ke gabansa.

Zulum, ya kuma gargadi cewa ba za a amince wani sarki ya rika mulkar jiharsa daga kasar waje ba.

Gwamna Zulum ya shaidawa sabon sarkin cewa masu nadin sarakuna na masarautar Bama ne suka bayar da shawarar a nada shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel