Mutum 100 sun mutu cikin sati daya a Bauchi

Mutum 100 sun mutu cikin sati daya a Bauchi

A kalla mutane 100 ne suka mutu a garin Azare da ke jihar Bauchi a makon da ta gabata inda suka yi fama da rashin lafiya mai alamomi da ke kama da na masu ciwon coronavirus.

Azare ne gari mafi girma a jihar bayan Bauchi, babban birnin jihar

Ibrahim Mohammed Baba, tsohon dan majalisar tarayya mai wakiltan Katagum ne ya bayyana hakan cikin wata wasikar neman taimako da ya aike wa Shugaba Muhammadu Buhari kamar yadda SaharaReporters ta ruwaito.

Baba ya ce mace macen da ake zargin COVID-19 ce ta yi sanadi ya jefa alummar garin cikin tashin hankali da damuwa.

Mutum 100 sun mutu cikin sati daya a Bauchi
Mutum 100 sun mutu cikin sati daya a Bauchi. Hoto daga Google
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Masu jinyar korona sun kule likitoci a cibiyar killacewa a Kano

Tsohon dan majalisar ya ce kusancin garin na Azare da Bauchi, Kano da wasu manyan garuruwa a Jigawa ya saka ta cikin hatsarin kamuwa da cutar.

Ya ce, "Kusancin Azare da Bauchi, Kano da wasu manyan birane a Jigawa ya saka alummar garin cikin hatsarin kamuwa da cutar duba da cewa ta yadu a sauran garuruwan.

"Saboda haka, ina kira ga shugaban kasa ya umurci Hukumar kiyayye cututtuka masu yaduwa, NCDC, da kwamitin shugaban kasa na yaki da COVID-19 su kai wa Azare dauki cikin gaggawa.

"Kazalika, ina son tunatar da kai cewa akwai sashin kula da ciwon ido da dakin gwaji da Bankin Kasa ta gina a Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Azare tun 2013 amma ba a kaddamar da shi ba har yanzu.

"Ana iya fara amfani da shi a sauya shi zuwa cibiyar killace da yi wa masu COVID-19 magani a kuma sayo kayayyakin da ake bukata kamar su Ventalator.

"Duba da cewa wannan harka ce ta rai, ina fata saboda kishin kasa da kaunar kiyaye lafiyar yan Najeriya za ka taimaka wa mutanen Azare da kewaye a magance wannan matsalar."

Idan ba a manta ba, tsohon Alkali, Justice Dahiru Saleh wanda ya yanke hukuncin soke zaben Juna 12 a 1993 ya mutu a ranar Alhamis a Azare.

Rahotanni sun ce coronavirus ce ta yi sanadin rasuwarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel