Dokar kulle: Limamai za su share gidan hakimi na sati daya a Kano

Dokar kulle: Limamai za su share gidan hakimi na sati daya a Kano

Kotun tafi da gidanka a jihar Kano na hukunta wadanda suka saba dokar kulle da aka kafa sakamakon bullar COVID-19 ta zartar da hukunci a kan wasu limamai biyu da aka samu da laifin saba dokar.

An yanke wa limaman biyu hukuncin share gidan hakimi har na tsawon kwanaki bakwai kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Baba Jibo Ibrahim, Cif Rajistara na jihar Kano ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Jumaa 9 ga watan Mayu.

Dokar kulle: Limamai za su share gidan hakimi na sati daya a Kano
Dokar kulle: Limamai za su share gidan hakimi na sati daya a Kano. Hoto daga jaridar Guardian
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Masu jinyar korona sun kule likitoci a cibiyar killacewa a Kano

A cewarsa, lamarin ya faru ne a karamar hukumar Minjibir na jihar.

Kotun ta yanke hukuncin cewa limamen su rika share gidan hakimin Minjibir na tsawon sati daya baya da tarar Naira 10,000.

Ya kara da cewa a lokacin da suke gudanar da wannan aikin, jamian karamar hukumar za su rika zuwa suna duba su domin tabbatar da cewa sun aikata aikin yadda ya dace.

A wani rahoton, kun ji cewa Farfesa Abdulrazak Habib, Shugaba a kwamitin kar ta kwana na yaki da COVID-19 a Kano, ya bayyana irin halin da ya shiga bayan kamuwa da korona da kuma yadda aka masa magani ya warke.

A ranar Alhamis 7 ga watan Mayu ne aka sallami Habib da wasu mambobin kwamitin na kar ta kwana da suka kamu da cutar tun ranar 17 ga watan Afrilu bayan sun warke.

Farfesan da ke aiki a Asibitin Koyarwa ta Aminu Kano da Jamiar Bayero ya ce an bashi magunguna da yawa da suka hada da "ruwan magani da aka saka masa ta jijiyoyi, iskar oxygen da siracen habbatus sauda da aka rika shaka masa, shayin chitta da wasu abubuwan."

An sanar da wannan bayanan ne a shafin Twitter na Ma'aikatar Lafiya na jihar a ranar Alhamis. Sanarwar ta ce, "Ina farin cikin sanar da ku cewa an sallame ni daga cibiyar killace masu COVID-19 na Kano bayan gwajin da aka yi min ya nuna na warke kuma kusan dukkan alamomin cutar sun gushe.

"Na kamu da cutar ne lokacin da na ke aiki a kwamitin kar ta kwana na COVID-19 a jihar.

"Na yi fama da zazzabi, tari, sarkewar munfashi, amai, gudawa, mutuwar jiki, rashin iya cin abinci da sauransu. Na yi fama da ciwo na wata daya kuma an killace ni na kwanaki 20.

Ya jadadda cewa akwai bukatar maaikatan lafiya su wayar da kan mutane game da COVID-19 kuma su kiyayye dukkan sharrudan kare kai daga kamuwa daga cutar kamar guje wa cinkoso da amfani da takunkumin fuska.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel