'Yan bindiga 200 sun kai hari, sun yi wa kauyuka 6 a Katsina mummunar barna

'Yan bindiga 200 sun kai hari, sun yi wa kauyuka 6 a Katsina mummunar barna

- Sama da 'yan bindiga 200 ne suka tsinkayi kauyuka 6 na karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina

- Kauyukan da 'yan bindigar suka hara sun hada da sugunni, Yandaka, Salihawar Duba, Garin Goje, Watangadiya da Dutse maizane

- 'Yan bindigar sun yi nasarar halaka wani Alaramma Kabiriu Kano mai shekaru 57 a kauyen Goje da ke jihar

Sama da 'yan bindiga 200 dauke da miyagun makamai da suka hada da bindigogi kirar AK 47 suka kai hari kauyuka 6 na karamar hukumar Batsari da ke jihar Katsina.

Kauyukna sun hada da Tsugunni, Yandaka, Salihawar Duba, Garin Goje, Watangadiya da Dutse maizane inda aka hara a lokaci daya, gidan talabijin din Channels ya ruwaito.

A yayin da aka kai harin a daren Alhamis, an gano cewa 'yan bindigar sun dinga harbi. Sun yi nasarar kashe wani Alaramma Kabiru Kano mai shekaru 57 a kauyen Garin Goje.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Gambo Isah, ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata takarda da ya fitar.

SP Gambo Isah ya kara da cewa, mutum uku ne suka samu miyagun raunika a kauyen Dutse Maizane.

Ya kara da cewa, shanaye da tumaki masu yawa wadanda basu kirguwa ne 'yan bindigar suka yi awon gaba dasu.

'Yan bindiga 200 sun kai hari, sun yi wa kauyuka 6 a Katsina mummunar barna
'Yan bindiga 200 sun kai hari, sun yi wa kauyuka 6 a Katsina mummunar barna. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa kanin Malam Mamman Daura rasuwa

'Yan bindigar sun kai harinsu har kan jami'an sojin Najeriya na hadin guiwa da 'yan sanda, wanda hakan ya kawo musayar wuta.

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon ta'aziyyarsa ga danginsa da kuma jama'ar garin Daura bayan rasuwar dan shi na dangi, Alhaji Murtala Dauda.

Alhaji Murtala Dauda kani ne ga Malam Mamman Daura, babban shakiki kuma aminin shugaban kasa Muhammadu Buhari. A wata takarda da ta fita daga hannun babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, Garba Shehu ya ce mutuwa rigar kowa ce kuma kowa sai ya dandanata.

Ya ce, "A madadina da na iyalaina, ina mika sakon ta'aziyyata a kan rashin Muntari Dauda.

"Mutuwa na kan kowa kuma babu mai guje mata. Kowacce rai za ta dandana mutuwa wata rana.

"Ba kukanmu mamatanmu ke so ba saboda hawayenmu ba zai dawo da su ba. Abinda suke bukata shine addu'a.

"A don haka nake ta'aziyya ga jama'ar garin Daura gaba daya a kan wannan babban rashin."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: