Coronavirus: An sallami mutum 42 da suka warke a jihar Legas

Coronavirus: An sallami mutum 42 da suka warke a jihar Legas

Gwamnatin jihar Legas ta sanar da sallamar mutane 42 daga cibiyar killacewa masu jinya bayan gwaji biyu daban-daban sun nuna cewa sun samu waraka daga cutar ta korona.

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, sanarwar hakan ta fito ne daga ma'aikatar lafiyar jihar cikin wani sako da ta wallafa kan shafinta na Twitter a ranar Juma'a.

Sanarwar ta bayyana cewa, mutanen da aka sallama daga cibiyoyin killacewa uku na jihar sun hadar da mata 20 da maza 22.

Ta yi bayanin cewa, an sallami mutum biyu daga cibiyar killacewa ta Onikan, 32 daga cibiyar Eti-Osa, sai kuma mutum takwas cibiyar Ibeju-Lekki.

A halin yanzu jimillar mutanen da aka sallama a jihar bayan samun waraka daga cutar korona sun kai 448 kamar yadda alkaluman ma'aikatar lafiyan jihar suka tabbatar.

Ya zuwa daren ranar Alhamis da ta gabata, alkaluman hukumar dakile cututtuka masu yaduwa a kasa NCDC sun nuna cewa, jihar Legas na da adadin mutane 1,491 da cutar korona ta harbu.

Mutum 30 cutar korona ta hallaka a jihar Legas kawo yanzu.

Kwamishinan lafiyar jihar Legas; Akin Abayomi

Kwamishinan lafiyar jihar Legas; Akin Abayomi
Source: Twitter

Taskar bayanai ta NCDC ta fitar da cewa, har ila yau, jihar Legas ce a kan sahu na gaba da mafi yawan adadin mutane da cutar korona ta harba cikin dukkanin jihohin da cutar ta bulla a kasar.

Babu shakka an samu bullar cutar a dukkanin jihohin kasar da kuma babban birnin tarayya in banda Kogi da Cross River.

KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa kotun koli ta sallami Orji Kalu daga gidan gyara hali

Alkaluman NCDC na ranar Alhamis, 7 ga watan Mayu, sun nuna cewa cutar korona ta harbi mutane 3526 yayin da tuni mutum 601 suka warke tun bayan bullarta a kasar.

A makon nan ne dai gwamnatin jihar Kogi ta ce ta gano tuggun da ake kullawa na neman ta dole sai an shigo da kwayoyin cutar korona cikin jihar ta kowace irin haramtacciyar hanya.

Gwamnatin jihar ta ce wannan yana daya daga cikin makarkashiyar da ake kulla wa na neman sai an tursasawa kowace jiha a fadin Najeriya samun bullar cutar.

Sai dai kwamishinan lafiya na jihar Kogi, Dr Saka Haruna, ya bayyana cewa, duk da huro wutar da ake yi wa gwamnatin jihar gami da matsin lamba, ba za ta yi karyar bullar cutar korona ba a jihar.

Kwamishinan ya ce duk wata tilastawa da wani matsin lamba, ba zai sa gwamnatin Kogi ta ayyana bullar cutar korona ba alhalin babu cutar a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel