An samu bullar annobar COVID-19 a yankunan karkara – Gwamna El-Rufai

An samu bullar annobar COVID-19 a yankunan karkara – Gwamna El-Rufai

Gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya bayyana damuwarsa game da karuwar matsalolin cutar COVID1-19 a yankunan karkara a jahar.

Daily Trust ta ruwaito gwamnan ya danganta yaduwar cutar ga tafiye tafiyen da jama’a suke yi, duk da haramcin da gwamnati ta yi a kan hakan, wanda hakan barazana ne ga al’ummar jahar.

KU KARANTA: Hukumar FIFA ta amince da canjin yan wasa 5 yayin wasan kwallon kafa

A ranar Juma’a, 8 ga watan Mayu ne gwamnan ya bayyana haka, inda yace yawancin masu cutar a Kaduna suna da tarihin tafiye tafiye, kuma hakan ne kara yaduwar cutar a Kaduna.

A cewar gwamnan, yawancin masu cutar sun fito ne daga kananan hukumomin Giwa, Igabi, Kaduna ta Arewa, Kaduna ta kudu, Makarfi, Soba da Zaria.

An samu bullar annobar COVID-19 a yankunan karkara – Gwamna El-Rufai

Gwamna El-Rufai Hoto: Shafin Giwa
Source: Facebook

Daga cikin sabbin mutane 7 da suka kamu da cutar a jahar, hudu matafiya ne da suka dawo daga wajen Kaduna, daya kuma babban mutumi ne dake samun ziyarar baki dayawa.

Sai kuma sauran mutane biyu wanda mazauna barikin Yansanda ne, kuma sun kamu ne sakamakon mu’amala da suka yi da wani jami’in Dansanda da ya kamu da cutar.

Don haka kwamitin yaki da cutar a Kaduna ta yi kira ga jama’a su dinga lura tare da ankara da duk wanda suka san daga tafiya ya dawo, saboda rashin haka na mayar da hannun agogo baya.

A wani labarin kuma, Hukumar kiwon lafiya ta majalisar dinkin duniya, WHO. ta bayyana cewa mutane 190,000 a Afirka za su iya mutuwa a sakamakon Coronavirus idan ba’a bi a hankali ba.

Premium Times ta ruwaito WHO ta bayyana haka ne a ranar Alhamis yayin da take gabatar da rahoton binciken da ta gudanar game da yaduwar annobar a yankin Afirka.

“Tsakanin mutane 83,000 zuwa 190,000 za su mutu a nahiyar Afirka daga cutar COVID-19, kuma tsakanin mutane miliyan 29 zuwa miliyan 44 za su kamu daga cutar a shekarar farko idan har ba’a dauki matakan dakatar da yaduwarta ba.” Inji ta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Online view pixel