Masu jinyar korona sun kule likitoci a cibiyar killacewa a Kano

Masu jinyar korona sun kule likitoci a cibiyar killacewa a Kano

Wani abu mai kama da wasan kwaikwayo ya faru a Kano a ranar Alhamis inda wasu masu jinyar cutar COVID-19 suka kulle wasu maaikatan lafiya a cibiyar killacewa ta Kwanar Dawaki da ke jihar.

Aminu Mohammed, tsohon shugaban kungiyar likitoci (NMA), reshen jihar Kano ne ya bayyana hakan yayin hira da aka yi da shi a shirin gidan rediyo a ranar Jumaa kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Ya ce masu jinyar da suka fusatta sun rufe maaikatan lafiyan likitoci biyu da malamar jinya daya a lokacin da suka shiga dakin masu jinyar don duba su kamar yadda suka saba.

Masu jinyar korona sun kule likitoci a cibiyar killacewa a Kano
Gwamna Ganduje da tawagar ma'aikatan lafiya. Hoto daga Gwamnatin Kano
Asali: UGC

DUBA WANNAN: COVID-19: Kasashe 5 da korona ta shiga amma ba ta yi kisa ba

Ya ce majinyatan sun rufe maaikatan lafiyar a wani daki na awanni.

Mohammed ya ce duk da fama da kallubalen rashin isasun kayan kare kai daga kamuwa da cuta (PPEs) da maaikatan lafiyan ke fuskanta suna cigaba da kula da marasa lafiyan.

Ya yi kira ga alumma su rika bawa likitoci da malaman jinya goyon baya da hadin kai ba wai musguna musu ba yayin gudanar da aikin su.

Daya daga cikin masu jinyar da ke cibiyar killacewar ya kira waya a yayin shirin na rediyo inda ya yi karin haske a kan abinda ya faru.

Majinyacin da bai fadi sunansa ba ya tabbatar wa gidan rediyon afkuwar lamarin.

Ya ce sun aikata hakan ne domin nuna rashin jin dadinsu kan rashin kulawa da su da kuma tsaiko da ake samu wurin yi musu gwaji da sanar da su sakamakon gwajin bayan sun shafe kwanaki suna shan magani.

Da aka tuntube shi, Shugaban kwamitin kar ta kwana na yaki da COVID-19 a Kano, Tijjani Husaini ya ce ba shi da masaniya game da afkuwar lamarin.

A halin yanzu korona ta kama mutane 482 a jihar ta Kano, hakan na nuna ita ce jiha ta biyu da tafi yawan masu cutar bayan Legas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel