Yadda wata mata ta haihu a titin jihar Legas (Hotuna)

Yadda wata mata ta haihu a titin jihar Legas (Hotuna)

- Runduna ta musamman ta jami'an tsaron jihar Legas ta ceci wata mata da ta haihu a kan titin Lekki da ke jihar Legas

- Kamar yadda ganau suka bayyana, matar ta fara zubar jini wanda ke nuna alamar nakuda a titin tare da yaranta hudu kanana

- An tuntubi runduna ta musamman ta jami'an tsaron wadanda suka garzaya da motarsu tare da mika ta asibiti da jaririyarta

Jami'an runduna ta musamman ta jihar Legas a safiyar Juma'a sun ceto wata mata da ta haihu a kan titin Lekki da ke jihar Legas.

Matar mai suna Deborah ta haifa diyarta mace wajen karfe 7 na safe a gaban wata babbar coci da ke Lekki.

Yadda wata mata ta haihu a titin jihar Legas (Hotuna)
Yadda wata mata ta haihu a titin jihar Legas (Hotuna). Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

An gano cewa matar tana tare da yaranta hudu kanana yayin da ta fara nakuda, jaridar The Nation ta wallafa.

An gano cewa zubar jinin da matar ke yi ne ya janyo hankulan masu wucewa wadanda suka hada da likitoci har suka taimaka mata.

Kamar yadda majiyar ta bayyana, an sanar da motar sintiri ta runduna ta musamman, bayan aukuwar lamarin kuma jami'an sun gaggauta zuwa daukar matar.

Bayan isar jami'an, sun dauka matar zuwa asibitin Eti-Osa na gwamnati da ke garin Ikate-Elegushi don samun a duba lafiyarta.

Yadda wata mata ta haihu a titin jihar Legas (Hotuna)
Yadda wata mata ta haihu a titin jihar Legas (Hotuna). Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kano: Yadda aka yi min maganin korona – Shugaban kwamitin kar ta kwana

Yadda wata mata ta haihu a titin jihar Legas (Hotuna)
Yadda wata mata ta haihu a titin jihar Legas (Hotuna). Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

An gano cewa matar ba ta da gida kuma bata da miji.

"Matar ba ta da gida kuma mahaifiyar yara hudu ce. Bata da miji amma muna farin cikin ganinta da jaririyar cikin koshin lafiya.

"Likitoci biyu ne suka raka kungiyar sintirin zuwa asibiti. Mutane da yawa sun dinga tururuwar kawo kayan mahaifiyar da kuma na jinjirar.

"Muna fatan gwamnati da mutane masu fadi a ji su kawo tallafi ga matar da yaranta don su bar titi," majiyar tace.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa jami'an sun ci gaba da samun jinjina tare da yabon jama'a a kan taimakon da suka yi.

Jami'an rundunar, karkashin jagorancin mataimakin kwamishinan 'yan sandan jihar, DCP Tunji Disu sun saba irin wannan taimakon.

Yadda wata mata ta haihu a titin jihar Legas (Hotuna)
Yadda wata mata ta haihu a titin jihar Legas (Hotuna). Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel