Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa kanin Malam Mamman Daura rasuwa

Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa kanin Malam Mamman Daura rasuwa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon ta'aziyyarsa ga danginsa da kuma jama'ar garin Daura bayan rasuwar dan shi na dangi, Alhaji Murtala Dauda.

Alhaji Murtala Dauda kani ne ga Malam Mamman Daura, babban shakiki kuma aminin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A wata takarda da ta fita daga hannun babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, Garba Shehu ya ce mutuwa rigar kowa ce kuma kowa sai ya dandanata.

Ya ce, "A madadina da na iyalaina, ina mika sakon ta'aziyyata a kan rashin Muntari Dauda.

"Mutuwa na kan kowa kuma babu mai guje mata. Kowacce rai za ta dandana mutuwa wata rana.

"Ba kukanmu mamatanmu ke so ba saboda hawayenmu ba zai dawo da su ba. Abinda suke bukata shine addu'a.

"A don haka nake ta'aziyya ga jama'ar garin Daura gaba daya a kan wannan babban rashin.

"Allah ya gafarta masa, yasa aljanna makoma gareshi, Ameen"

Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa kanin Malam Mamman Daura rasuwa

Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa kanin Malam Mamman Daura rasuwa. Hoto daga Daily Nigerian
Source: Twitter

KU KARANTA: Rasuwar mahaifiyar Buratai: Kalaman da Zulum ya yi ga babban hafsin sojan

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya jajanta wa shugaban hafsin sojan Najeriya, Laftanal Janar Tukur Buratai a kan rasuwar mahaifiyarsa, Hajia Hauwa a Maiduguri.

Mahifiyar Buratai ta rasu a ranar Talatar da ta gabata ne bayan jinyar da ta yi a asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri inda aka kwantar da ita. Sakon ta'aziyyar Gwamna Zulum ga Buratai ya fito a daren Alhamis ta hannun kakakinsa, malam Isa Gusau.

"Za a tuna mahaifiyarmu Kaka Hajja sakamakon sadaukarwar da ta yi wa Najeriya. Ta haifa daya daga cikin jarumai kuma sadaukan hafsin sojan kasar nan.

"Dan ta kuma dan uwanmu dan asalin jihar Borno, Laftanal Janar Tukur Buratai ya zama abun alfaharinmu a Borno da Najeriya baki daya.

"Da albarkar Hajja Kaka tare da kulawarta ne har Buratai ya shiga rundunar soji kuma ya kasance na sahun gaba wajen yakar 'yan ta'addan Boko Haram," yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel