Dalilin da ya sa kotun koli ta sallami Orji Kalu daga gidan gyara hali

Dalilin da ya sa kotun koli ta sallami Orji Kalu daga gidan gyara hali

Cikin wani yanayi na bazata, a ranar Juma'a 8 ga watan Mayu, kotun koli ta soke hukuncin da aka yankewa tsohon gwamnan jihar Abia, Sanata Orji Uzor Kalu.

Kotun kolin ta soke hukuncin daurin shekaru 12 da wata babbar kotun tarayya ta shimfida wa Orji Kalu wanda ya kasance wakilin shiyyar Abiya ta Arewa a majalisar dattawa.

A watan Dasumban shekarar da ta gabata ne, babbar kotu ta zartar da hukunci a kan tsohon gwamnan.

Bayan ta gamsu da zarginsa da almundahana, kotun ta yankewa Orji da wasu mutum biyu da laifin karkatar da kimanin biliyan 7.1 na dukiyar gwamnatin jihar Abia.

Sai dai fa a yanzu duk da ya shaki iskar 'yanci yayin da kotun kolin ta warware hukuncin da babbar kotun zartar, ta kuma umarci a sake masa sabuwar shari'a.

Kamar yadda jaridar Premium Times ta tabbatar, a yanzu haka Mista Orji ya koma gidansa da ke cikin fadar shugaban kasa a titin Queen Amina bayan ya fito daga gidan gyaran hali da ke Kuje a birnin Abuja.

Kwamitin Alkalai bakwai na kotun kolin karkashin jagorancin Jastis Amina Augie, sun yanke hukucin cewa, babbar kotun tarayya ta Legas wadda ta yi shari'ar a baya, hukuncinta bai inganta ba.

Sanata Orji Uzor Kalu

Sanata Orji Uzor Kalu
Source: UGC

A hukuncin da kotun kolin ta zartar da safiyar yau Juma'a ta riki cewa, Jastis Muhammad Liman, wanda ya yanke hukuncin bai kasance alkalin babbar kotun tarayyar ba a lokacin da ya yi zaman yanke hukunci kan tsohon gwamnan.

A cewar kotun kolin, Jastis Liman bai da ikon dawowa ya zauna a matsayin alkalin babbar kotun, kasancewar an riga da yi masa karin matsayi zuwa alkalin kotun daukaka kara kafin wannan lokacin.

KARANTA KUMA: Jihohi 35 da aka samu bullar cutar Covid-19 a Najeriya - NCDC

A tanadin sakin layi na 7 cikin sashe na 397 a kundin tsarin shari'a, an bai wa kowane alkali da aka kara wa matsayi zuwa kotun daukaka kara damar da zai sake dawo wa babbar kotu domin jagorantar shari'a har da ma zartar da hukunci.

Da ya ke kuma shari'a sabanin hankali musamman yadda duk wani hukunci da kotun koli ta zartar a baya ya ke kasancewa hujja da kuma madogara ta zartar da wani makamancin hukuncin a lokaci na daban.

Mun ji cewa a yanzu kotun kolin ta yi amfani da irin wannan dama wajen warware hukuncin da babbar kotun ta zartar a kan tsohon gwamnan.

Ta buga hujja da wata karar da aka shigar a tsakanin Ogbuanyinya da wasu mutum biyar a bangare daya da kuma V. Obi Okudo da wasu mutum uku a daya bangaren a shekarar 1979.

Kotun kolin a ranar 17 ga watan Yuni na shekarar 1977, ta soke hukuncin da Alkali Nnaemeka-Agu ya yanke bisa dalilin cewa an riga da kara masa matsayi daga alkalin babbar kotu zuwa na kotun daukaka kara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel