Yanzu-yanzu: Kimanin mutane 120,000 zasu kamu da Coronavirus nan da watanni 2 a Legas kadai

Yanzu-yanzu: Kimanin mutane 120,000 zasu kamu da Coronavirus nan da watanni 2 a Legas kadai

Kwamishanan lafiyan jihar Legas, Akin Abayomi, ya ce nan da watan Yuli zuwa Agusta, za a samu kimanin kamuwar mutane 120,000 da Coronavirus a jihar.

Ya bayyana hakan ne a hirar da yayi da manema labarai ranar Juma'a.

Kwamishanan ya ce dubi ga yadda ake samun karuwan masu cutar a jihar Legas, akwai yiwuwan adadin zai yi tashin gwauron zabo nan da watanni biyu.

Yace “Wata daya baya yanzu, ranar 7 ga Afrilu, mutane 10 ke kamuwa a rana. Bayan makonni biyu mutane 32 ke kamuwa, sai ta tashi 70. Yanzu mutane 100 ke kamuwa kulli yaumin.,”

“Ko shakka babu bamu kusa kawowa karshen lamarin ba, muna kyautata zaton zai hau nan da Yuli ko agusta kuma a shirye muke.”

Nan da ranar Jumaa, jihar na da adadin Vasu Korona 1,491 amma kwamishanan ya ce baccin matakan da gwamnatin ta dauke, da yanzu mutane 6000 suka kamu yanzu.

KU KARANTA Almajiranci ba ya amfanar Almajirai, ba ya amfanar Najeriya inji El-Rufai

Yanzu-yanzu: Kimanin mutane 120,000 zasu kamu da Coronavirus nan da watanni 2 a Legas kadai
Farfesa abayo
Asali: Twitter

A wani labarin daban, Karo na biyu cikin mako daya, masu fama da cutar Korona a jihar Gombe sun sake gudanar da zanga-zanga kan rashin kyakkyawawan kula da ake basu duk da suna killace.

Wani mazaunin jihar da aka sakaye sunansa ya bayyanawa TheCable ranar Jumaa cewa abinda gwamnatin jihar tayi ya sa suka sake fitowa zanga-zanga yau.

Yace “Bayan zanga-zangan ranar Talata, gwamnatin ta ji kunya, saboda haka ta mayar da hankali kan wadanda ke kwance a cibiyar killacewar garin Kwandon, inda ta manta da wadanda ke asibiti suna tunanin cewa jamian asibitin zasu iya kwantar da hankalinsu.”

Amma yayinda marasa lafiyan dake asibtin suka samu labarin cewa an inganta abubuwa a dayan wajen, sun fusata saboda sun ji gwamnati ta manta da su ne saboda basu yi zanga-zanga (kamar yadda na can sukayi ba.)”

”Saboda haka suke zanga-zanga a yau, suna tayar da hankulan mutane har sai lokacin da jamian tsaron suka samu nasarar tarwatsa su.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel