Zamfara: Matawalle ya kori sakataren hukumar Zakka da wasu daraktoci 2

Zamfara: Matawalle ya kori sakataren hukumar Zakka da wasu daraktoci 2

Gwamnatin jihar Zamfara ta sallami sakataren hukumar zakka ta jihar tare da wasu daraktoci biyu a take.

Wannan hukuncin ya biyo bayan taron da shugaban hukumar tare da mambobin amintattu na hukumar ta yi a ranar Juma'a.

A yayin zantawa da manema labarai a garin Gusau, shugaban hukumar, Farfesa Kabiru Jabaka ya ce mambobin hukumar ne suka bayyana cewa wasu daga cikin ma'aikatan hukumar na zagon kasa a bangaren raba Zakka da karfafa marasa hali.

Jabaka ya bayyana cewa daga cikin mambobi 15, 13 daga ciki sun samu shaida mai kyau.

Sakataren hukumar, Mallam Bashir Surajo da daraktocinsa biyu; Mallam Ibrahim Tudu da Mallam Dalhatu Jauri ne basu samu ba.

Kamar yadda shugaban hukumar ya bayyana, wa'adin aikin sakataren hukumar ya cika.

"Kamar yadda muka yanke hukunci, mun amince da sauwake wa sakataren da daraktocinsa biyu aikinsu, wa'adinsu ya cika," yace.

Zamfara: Matawalle ya kori sakataren hukumar Zakka da wasu daraktoci 2

Zamfara: Matawalle ya kori sakataren hukumar Zakka da wasu daraktoci 2 Hoto daga The Cable
Source: Twitter

KU KARANTA: Rasuwar mahaifiyar Buratai: Kalaman da Zulum ya yi ga babban hafsin sojan

A don haka ne hukumar ta nada Aliyu Musa Mafara wanda zai yi aiki a matsayin mukaddashin sakataren hukumar har zuwa lokacin da za a nada wani.

Farfesa Jabaka ya tabbatar wa da gwamnatin jihar Zamfara cewa dukkan mambobin hukumar za su tabbatar da nasarar hukumar a jihar.

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya jajanta wa shugaban hafsin sojan Najeriya, Laftanal Janar Tukur Buratai a kan rasuwar mahaifiyarsa, Hajia Hauwa a Maiduguri.

Mahifiyar Buratai ta rasu a ranar Talatar da ta gabata ne bayan jinyar da ta yi a asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri inda aka kwantar da ita. Sakon ta'aziyyar Gwamna Zulum ga Buratai ya fito a daren Alhamis ta hannun kakakinsa, malam Isa Gusau.

"Za a tuna mahaifiyarmu Kaka Hajja sakamakon sadaukarwar da ta yi wa Najeriya. Ta haifa daya daga cikin jarumai kuma sadaukan hafsin sojan kasar nan.

"Dan ta kuma dan uwanmu dan asalin jihar Borno, Laftanal Janar Tukur Buratai ya zama abun alfaharinmu a Borno da Najeriya baki daya.

"Da albarkar Hajja Kaka tare da kulawarta ne har Buratai ya shiga rundunar soji kuma ya kasance na sahun gaba wajen yakar 'yan ta'addan Boko Haram," yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel