Jihohi 35 da aka samu bullar cutar Covid-19 a Najeriya - NCDC

Jihohi 35 da aka samu bullar cutar Covid-19 a Najeriya - NCDC

Kawo yanzu an samu bullar cutar korona a jihohi 35 na Najeriya ciki har da babban birnin tarayya kamar yadda kididdigar hukumar dakile cututtuka masu yaduwa a kasar NCDC ta tabbatar.

Babu shakka hukumomin lafiya na ci gaba fadi-tashi domin dakile yaduwar cutar coronavirus a Najeriya, sai dai fa lamarin ya ci tura domin kuwa cutar na ci gaba da bazuwa a kasar.

Taskar bayanai ta NCDC a ranar Alhamis, 7 ga watan Mayun 2020, ta ce cutar korona ta harbi mutane 3526 yayin da tuni mutum 601 suka warke tun bayan bullarta a kasar.

Jadawalin NCDC ya tabbatar da cewa ya zuwa yanzu dai cutar corona ta hallaka mutum 107 a fadin kasar.

KARANTA KUMA: Kusan duk wadanda cutar korona ta kama za su warke - NCDC

Da misalin karfe 11.32 na daren ranar Alhamis, NCDC ta sanar da cewa an samu karin mutane 381 da cutar ta harba a fadin Najeriya.

Sabbin mutane 381 da cutar ta harba cikin jihohin 18 states sun kasance kamar haka: Lagos(183), Kano(55), Jigawa(44), Zamfara(19), Borno(9), Bauchi(19), Katsina(11), Kwara(8), Kaduna(7), Gombe(6), Ogun(5),Sokoto(4), Oyo(3), Rivers(3), Niger(2), Akwa Ibom(1), Enugu(1), Plateau(1).

Har ila yau jihar Legas ce a kan sahu na gaba ta fuskar yawan mutanen da cutar ta harba, sai kuma jihar Kano a mataki na biyu yayin da birnin tarayya Abuja ya biyo bayansu a mataki na uku.

Ga jerin adadin mutanen da suka kamu da cutar a kowace daya daga cikin jihohi 35 na Najeriya da cutar ta bulla:

Lagos-1,491; Kano-482; Abuja-316; Ogun-100; Gombe-109; Osun-37; Katsina-106; Borno-125; Edo-65; Oyo-55; Kaduna-92; Bauchi-102; Akwa Ibom-17; Kwara-24; Sokoto-89; Ekiti-12; Ondo-13; Rivers-17; Delta-17; Taraba-15; Jigawa-83; Enugu-9; Niger-6; Abia-2; Zamfara-65; Benue-2; Anambra-1; Adamawa-15; Plateau-5; Imo-2; Bayelsa-5; Ebonyi-5; Kebbi-18; Nasarawa-11; Yobe-13.

Ga jerin adadin mutanen da cutar korona ta hallaka a jihohin Najeriya da cutar ta bulla:

Lagos (33), Abuja (4), Kano (13), Ogun (2), Kaduna (1), Akwa Ibom (8), Katsina (2), Sokoto (8), Edo (4), Borno (14), Ebonyi (1), Osun (4), Oyo (2), Ekiti (1), Delta (3), Rivers (2), Nasarawa (1), Yobe (1), Zamfara (3), Jigawa (1).

Sannan kuma ga jerin adadin mutanen da suka warke a jihohin Najeriya da cutar ta bulla:

Lagos (406), Kano (19), Abuja (40), Katsina(9), Ogun (18), Kaduna (14), Bauchi (6) Akwa Ibom (10), Kwara (8), Anambra (1), Edo (10), Ondo (6), Enugu (2), Osun (30), Oyo (11), Ekiti (2), Delta (2), Rivers (2), Sokoto (1), Neja (1), Plateau (1), Imo (1), Abia(1).

An samu bullar cutar korona cikin dukkanin jihohin Najeriya in banda jihar Kogi da kuma Cross River.

KARANTA KUMA: Baƙin ciki ya tunkaro jihohin Najeriya yayin da lalitar gwamnatin tarayya ta yi kasa

A makon nan ne dai gwamnatin jihar Kogi ta ce ta gano tuggun da ake kullawa na neman ta dole sai an shigo da kwayoyin cutar korona cikin jihar ta kowace irin haramtacciyar hanya.

Gwamnatin jihar ta ce wannan yana daya daga cikin makarkashiyar da ake kulla wa na neman sai an tursasawa kowace jiha a fadin Najeriya samun bullar cutar.

Ta yi zargin cewa "a baya-bayan nan akwai miyagun da ke ci gaba da matsin lamba ta lallai sai an lalubo masu cutar tare da kaddamar da bullar ta a jihar."

A rahoton da jaridar Premium Times ta ruwaito, gwamnatin Kogi ta yi zargin yadda wasu masu wannan mummunar bukata ke huro wutar ayyana samun bullar cutar a jihar.

Sai dai fa gwamnatin ba ta fayyace ainihin masu neman kulla tuggun da zai shuka wannan mummunar badakala ba.

Kwamishinan lafiya na jihar Kogi, Dr Saka Haruna, ya bayyana cewa, duk da huro wutar da ake yi wa gwamnatin jihar gami da matsin lamba, ba za ta yi karyar bullar cutar korona ba a jihar.

Kwamishinan ya ce duk wata tilastawa da wani matsin lamba, ba zai sa gwamnatin Kogi ta ayyana bullar cutar korona ba alhalin babu cutar a jihar.

Furuncin kwamishinan ya zo ne cikin wata sanarwar da ya gabatar wa manema labarai a ranar Alhamis kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Dr Haruna ya yi martani dangane da jita-jitar da ke yaduwa a jihar ta cewa ana zargin cutar korona ce ta kassara wasu mutane hudu da suka riga mu gidan gaskiya a cibiyar lafiya ta tarayya da ke Lakwaja, a cikin makon da ya gabata.

A cewarsa, dukkanin masu wannan matsin lamba a jihar, 'yan siyasa ne da ke adawa da gwamnatin jihar mai ci a yanzu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel