Mutuwa riga: Kwamishina a gwamnati jahar Taraba ya rigamu gidan gaskiya

Mutuwa riga: Kwamishina a gwamnati jahar Taraba ya rigamu gidan gaskiya

Gwamnatin jahar Taraba a karkashin jagorancin Gwamna Darius Ishaku ta sake tafka wani babbar rashi biyo bayan mutuwar kwamishinan jahar mai suna Naphtali Kefas.

Punch ta ruwaito gabanin mutuwarsa, Mista Naphtali Kefas, shi ne kwamishinan yaki da talauci a jahar Taraba, kuma ya rasu ne a ranar Alhamis, 7 ga watan Mayu.

KU KARANTA: Makashin maza: Sojoji sun halaka ‘Orjondu’ da suka dade suna farautarsa wurjanjan a Benuwe

Wannan it ace mutuwa ta biyu da aka samu a majalisar zartarwar jahar Taraba, inda bai wuce wata daya ba da kwamishinan rara karkara na jahar, Makus Senlo ya mutu a garin Yola ba.

Babban mashawarci na musamman ga gwamnan jahar Taraba a kan harkar watsa labaru, Bala Dan-Abu ne ya sanar da mutuwar kwamishina Kefas Naphtali.

Sanarwar ta ce mutuwar Naphtali ta zo ne yayin da bai cika ko shekara daya a majalisar zartarwa gwamnatin jahar ba.

“Mutuwa ta dauke ma jahar Taraba hazikin ma’aikaci kuma mutum mai kishin jama’ansa, marigayi Kefas mutum ne mai tausayi, shi yasa ma aka tura shi ma’aikatar yaki da talauci don ya taimaka ma gwamnati wajen aiwatar da manufofinta tare da baiwa talaka daman a dama da shi.” inji shi.

Daga karshe gwamnan ya yi fatan Allah Ya baiwa iyalansa, yan uwa da abokan arzikinsa da kuma kafatanin jama’an garin Wukari juriyan hakurin rashin da suka yi.

A wani labarin kuma, miyagu yan bindiga sun yi kutse a gidan wani magidanci dake kauyen Tarkende cikin garin Umenger, na karamar hukumar Guma a jahar Benuwe a daren Laraba.

A yayin wannan kutse da suka yi, sun kashe maigidan tare da matarsa wanda take dauke da juna biyu ta hanyar bude musu wuta, inda suka musu ruwan harsashi babu gaira babu dalili.

An ruwaito mazauna kauyen sun bayyana cewa suna barci karar harbin bindiga ya tashe su a firgice kowa ya yi ta kansa don neman tsira, a sanadiyyar haka yan bindiga sun jikkata wasu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel