Yanzu-yanzu: EFCC ta yi martani a kan sakin Sanata Orji Kalu daga gidan yari

Yanzu-yanzu: EFCC ta yi martani a kan sakin Sanata Orji Kalu daga gidan yari

A yau Juma'a, 8 ga watan Mayun 2020 ne kotun koli ta soke hukuncin shekaru 12 a gidan gyaran hali da wata babbar kotun tarayya ta yankewa Sanata Orji Kalu.

Duk da kotun kolin bata wanke shi daga zargin handamar kudaden da ake masa ba, kotun ta soke shari'ar tare da bukatar a sauya shari'ar.

Kotun ta dogara da cewa mai shari'a Mohammed Liman, wanda ya yanke hukuncin ya bar babbar kotun tarayyar a lokacin da ya yi hukuncin, kamar yadda EFCC ta wallafa a shafinta na twitter.

A wata takarda da ta fito daga hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta fitar, ta ce za ta sake gurfanar da Kalu da gaggawa.

EFCC ta kwatanta sabon hukuncin da kokarin farautar hukunta tsohon gwamnan.

"EFCC ta gano cewa kotun koli ta soke hukuncin da aka yankewa tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Kalu, kamfaninsa mai suna Slok Nigeria Limited da Jones Udeogu, tsohon daraktan kudi na jihar Abia tare da bada umarnin sabuwar shari'a," takardar tace.

Yanzu-yanzu: EFCC ta yi martani a kan sakin Sanata Orji Kalu daga gidan yari
Yanzu-yanzu: EFCC ta yi martani a kan sakin Sanata Orji Kalu daga gidan yari. Hoto daga The Punch
Asali: Facebook

KU KARANTA: COVID-19: Gwamna Yahaya Bello ya yi martanin da ya kori tawagar FG daga jiharsa

Kamar yadda takardar da ta fito daga kakakin EFCC, Dele Oyewale ta bayyana, "Kotun kolin ta dogara da cewa Jastis Mohammed Idris wanda ya yanke hukuncin ya koma kotun daukaka kara amma ya koma babbar kotun don yanke hukuncin.

"EFCC ba ta ji dadin abinda kotun kolin tayi ba kuma ta dauka hakan da kokarin zagon kasa ga hukuncin da aka yi wa tsohon gwamnan.

"Hukumar a shirye take da sake gurfanar da tsohon gwamnan saboda shaidunta bayyanannu ne.

"Shaidun almundahanar kudaden da take da su ne yasa kotun kolin ta kasa wanke shi. EFCC za ta sake gurfanar da shi har sai an tabbatar da adalci."

An gurafanar da Kalu a kan tuhumarsa da ake da laifuka 36 da suka hada da almundahanar kudi har naira biliyan 7.1.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel