Yadda wani magidanci da matarsa mai ciki suka gamu da ajalinsu a hannun yan bindiga

Yadda wani magidanci da matarsa mai ciki suka gamu da ajalinsu a hannun yan bindiga

Wasu gungun miyagu yan bindiga sun yi kutse a gidan wani magidanci dake kauyen Tarkende cikin garin Umenger, na karamar hukumar Guma a jahar Benuwe a daren Laraba.

A yayin wannan kutse da miyagun suka yi, sun kashe maigidan da matarsa wanda take dauke da juna biyu ta hanyar bude musu wuta, inda suka musu ruwan harsashi babu gaira babu dalili.

KU KARANTA: Miji ya watsa ma matarsa tafasashshen ruwan zafi a kan zarginta da cin amana

Daily Trust ta ruwaito mazauna kauyen sun bayyana cewa suna barci karar harbin bindiga ya tashe su a firgice kowa ya yi ta kansa don neman tsira, a sanadiyyar haka wasu sun jikkata.

Shugaban karamar hukumar Guma, Anthony Shawon ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace yan bindigan sun kashe miji da mata, sa’annan yan garin da dama sun jikkata.

Yadda wani magidanci da matarsa mai ciki suka gamu da ajalinsu a hannun yan bindiga
Hare hare a Benuwe Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Sai dai Shawon ya yi zargin yan bindigan makiyaya ne, saboda bayan harin sun yi awon gaba da wata mata, amma ta samu daman tserewa daga hannunsu, kuma ta koma gida.

“A yanzu da nake magana, Sarkin kauyen Ujaende yana tare da ni yana rokon na tura musu Sojoji domin su dinga sintiri a yankin don su samu daman zuwa gona, wannan shi ne halin da muke ciki a Guma gaba daya.” Inji shi.

Da aka tuntubi kakaakin Yansandan jahar, DSP Catherine Anene game da lamarin, sai ta ce sun samu rahoton harin, kuma suna hanyar zuwa inda lamarin ya auku don gane ma idanunsu.

A wani labari kuma, dakarun rundunar Sojin Najeriya dake jahar Benuwe sun samu nasarar halaka Terugwa Igbagwa, kasurgumin dan bindiga da suka dade suna farautarsa ruwa a jallo.

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito shugaban sashin watsa labaru na shelkwatar tsaro, Manjo Janar John Enenche ne ya bayyana haka a ranar Juma’a, 8 ga watan Mayu.

Enenche yace Terugwa Igbagwa inkiya Orjundu ya gamu da ajalinsa ne a wani hari da Sojoji suka kai a mafakar miyagun dake kan hanyar Zaki Biam zuwa Katsina-Ala a Benuwe.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: