Buhari ya nada Ali Hassan a matsayin shugaban riko na Bankin Manoma

Buhari ya nada Ali Hassan a matsayin shugaban riko na Bankin Manoma

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin Alwan Ali Hassan a matsayin Shugaban riko na Bankin Manoma, BoA.

Sanarwar mai dauke da sa hannun Direktan Sadarwa na Maaikatar Noma da Raya Karkara, Theodore Ogaziechi, ya fitar ranar Alhamis ta ce Shugaba Buhari ya amince da rushe kwamitin wucin gadi mai kula da bankin nan take.

Mr Hassan, kwararran ma'aikacin banki da ya yi aiki na fiye da shekaru 20 zai karbi ragamar jagorancin bankin manoman kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Buhari ya nada Ali Hassan shugaban riko na Bankin Manoma
Buhari ya nada Ali Hassan shugaban riko na Bankin Manoma. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Kano: Yadda aka yi min maganin korona – Shugaban kwamitin kar ta kwana

A cewar sanarwar, sanarwar nadin na cikin wasikar da Ministan Noma, Mohammad Nanono ya samu daga shugaban kasa mai lamba PRES/95/MARD/14.

Sanarwar ta kuma kara da cewa Mr Hassan dan asalin jihar Kano ne kuma yana da digiri na biyu a Fanin Kasuwanci sannan ya yi aiki a matsayin mamba na kwamitin amintattu na Orient Bank, Bank PHB da Platinum Capital and Trust Limited.

Shine kuma shugaban Midrange Universal Biz Ltd kuma mamba na Chartered Institute of Bankers da Nigerian Institute of Quantity Surveyors da wasu kungiyoyin.

Ya kuma samu horo a wasu fitattun makarantu na duniya da suka hada da MD Business School Lausanne, kasar Switzerland da Intrados Business School, Washington DC, Amurka.

BoA ce babban bankin manoma a kasar nan da ke da alhakin bayar da bashi da tallafi ga manoma da wasu ababen da za su inganta harkokin noma.

A wani rahoton, kun ci cewa jami'an tsaro sun hana dubban yan kasuwa da masu cin kasuwa shiga kasuwar sayar da tufaffi na Kwari da ke Kano a yayin da gwamnatin jihar ta sassauta dokar kulle da ta saka a baya don dakile yaduwar korona.

Idan za a tuna Gwamna Abdullahi Ganduje a makon da ya gabata ya sanar da cewa kasuwannin Yan Kaba da Yan Lemo ne kawai aka bawa damar budewa a ranakun Litinin da Alhamis.

An kuma bawa wasu manyan kantina damar budewa domin sayar wa alumma kayan masarafi a ranakun biyu daga karfe 10 na safe zuwa 4 na yamma.

An kuma dakatar da yin sallolin Jumaa da zuwa coci a ranakun Lahadi na kimanin sati uku da suka gabata a yunkurin da jihar ke yi na dakile yaduwar annobar ta korona.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164