Yanzu-yanzu: An saki Orji Uzor Kalu daga gidan yari

Yanzu-yanzu: An saki Orji Uzor Kalu daga gidan yari

Orji Uzor Kano, Sanata mai ci da aka tura kurkuku kan laifin almundahanan kudin jiharsa ya shaki iskar yanci yayinda aka sakeshi daga gidan yari.

Kalu, wanda tsohon gwamnan jihar Abiya ya samu fitowa daga gidan gyara halin dake Kuje, Abuja da safiyar Juma'a, Premium Times ta samu rahoto.

A yanzu haka, an garzaya da shi gidansa dake cikin fadar shugaban kasa a titin Queen Amina, majiyan sun tabbatar.

Majiyoyin sun bukaci a sakaye sunayensu saboda suna kusa da Orji Kalu kuma ba da izininsa suka fadawa yan jarida an sakeshi ba.

An saki Mista Kalu ne yan mintuna bayan kotun koli ya soke hukuncin daureshi na tsawon shekara 12 da aka yanke a watan Disamba, 2019.

Kotun koli, a ranar Juma’a, 8 ga watan Mayu, ta soke hukuncin da aka yankewa tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor-Kalu na shekaru 12 a gidan yari.

Kotun kolin, a wani hukunci da kwamitin alkalai bakwai karkashin jagorancin Justis Amina Augie suka yanke, sun riki cewa babbar kotun tarayya ta Lagas ta yanke hukunci ba tare da hurumin yin hakan ba.

Wajen hukunta Kalu, da kamfaninsa na Slok Nigeria Limited da kuma tsohon daraktan kudi na jihar Abia, Jones Udeogu.

Ta riki cewa Justis Mohammed Liman wanda ya yanke hukuncin bai kasance alkalin babbar kotun tarayyar ba a lokacin da ya yi zaman yanke hukunci kan wadanda ake karar.

Ana zarginsu da satan kudi kimanin naira biliyan 1.7 daga asusun jihar Abia.

A cewar kotun kolin, Justis Liman bai da ikon dawowa ya zauna a matsayin alkalin babbar kotu kasancewar an dauke shi zuwa kotun daukaka kara kafin wannan lokacin.

KU KARANTA: COVID-19: Gwamna ya yi umurnin yin gwanjon motocin da aka kama suna karya dokar kulle

Saboda haka, kotun kolin ta dage hukuncin da aka yankewa wadanda ake karan sannan ta yi umurnin sake sabon shari’a, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel