Rasuwar mahaifiyar Buratai: Kalaman da Zulum ya yi ga babban hafsin sojan

Rasuwar mahaifiyar Buratai: Kalaman da Zulum ya yi ga babban hafsin sojan

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya jajanta wa shugaban hafsin sojan Najeriya, Laftanal Janar Tukur Buratai a kan rasuwar mahaifiyarsa, Hajia Hauwa a Maiduguri.

Mahifiyar Buratai ta rasu a ranar Talatar da ta gabata ne bayan jinyar da ta yi a asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri inda aka kwantar da ita.

Sakon ta'aziyyar Gwamna Zulum ga Buratai ya fito a daren Alhamis ta hannun kakakinsa, malam Isa Gusau.

"Za a tuna mahaifiyarmu Kaka Hajja sakamakon sadaukarwar da ta yi wa Najeriya. Ta haifa daya daga cikin jarumai kuma sadaukan hafsin sojan kasar nan.

"Dan ta kuma dan uwanmu dan asalin jihar Borno, Laftanal Janar Tukur Buratai ya zama abun alfaharinmu a Borno da Najeriya baki daya.

"Da albarkar Hajja Kaka tare da kulawarta ne har Buratai ya shiga rundunar soji kuma ya kasance na sahun gaba wajen yakar 'yan ta'addan Boko Haram.

Rasuwar mahaifiyar Buratai: Kalaman da Zulum ya yi ga babban hafsin sojan
Rasuwar mahaifiyar Buratai: Kalaman da Zulum ya yi ga babban hafsin sojan. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: COVID-19: Gwamna Yahaya Bello ya yi martanin da ya kori tawagar FG daga jiharsa

"Jihar Borno ba za ta taba mantawa da Kaka Hajja da ta haifa wa Najeriya Buratai tare da saka mishi horarwa ta kishin kasa da sadaukantaka.

"Muna matukar jin kunar rashin Kaka Hajja tare da jajanta wa dan uwanmu Buratai da dukkan iyalansa.

"Muna fatan Allah ya yi mata rahama tare da yafe mata zunubbanta. Allah ya sanya ta a aljanna ya kuma ba iyalanta karfin jure wannan babban rashin da ba za a iya mayar da shi ba," Zulum ya ce a takardar.

A ranar Talata ne muka ji cewa, Allah ya yi wa Kakah Hajja, mahaifiyar babban hafsin sojojin Najeriya rasuwa a ranar Talata.

Wata majiya daga dangin su Buratai ya shaida wa Sahara Reporters cewa marigayiya Hajja ta rasu ne bayan tayi fama da gajeruwar rashin lafiya a gidan ta da ke Maiduguri a jihar Borno.

Majiyar ta ce, "Eh, tabbas ina tabbatar muku da cewa ta rasu.

"Ta rasu da yammacin yau kuma za a yi mata janaiza gobe da karfe takwas na safe.

"Allah ya jikan ta da rahama. Amin."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng